logo

HAUSA

A karon farko farin jinin Biden ya yi kasa da kaso 50 cikin 100

2021-08-19 11:05:48 CRI

A karon farko farin jinin Biden ya yi kasa da kaso 50 cikin 100_fororder_src=http___thumb.takefoto.cn_wp-content_uploads_2021_08_202108031009505653&refer=http___thumb.takefoto

Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a daban-daban da aka kada, sun nuna cewa, a karon farko matsakaicin farin jinin shugaba Biden na Amurka, ya yi kasa da kaso 50 cikin 100, tun lokacin da ya kama aiki zuwa yanzu.

Ya zuwa jiya Laraba, farin jinin shugaba Biden ya yi kasa zuwa kaso 49.3 cikin 100, cikin binciken jin ra’ayoyin jama’a da tashar Internet ta FiveThirtyEight ta gudanar, inda masu nuna rashin amincewa da kwazon shugabancinsa, ya kai kaso 44.2 cikin 100, adadin da ya karu kadan, daga sama da kaso 34 cikin 100 a karshen watan Janairu, lokacin da ya shiga fadar White House.

Alkaluma mafiya muni, su ne na kamfanin dillancin labarai na Reuters/Ipsos, wadanda ke nuna cewa, farin jinin Biden ya yi kasa, daga kaso 53 cikin 100 a ranar Jumma’ar da ta gabata zuwa kaso 46 cikin 100 a ranar Talata, abin da ke nuna cewa, hakan na da nasaba da rudanin dake faruwa a kasar Afghanistan, inda shugaban ya amince cewa, zai fuskanci suka, yayin da yake kare matsayin gwamnatinsa, game da janye dakarun kasar daga kasar Afghanistan.

A game da yaki da annobar COVID-19 kuwa, an kara samun masu kamuwa da annobar a Amurka. Yanzu haka, yawan sabbin masu kamuwa da cutar a cikin kasar, ya karu fiye da kaso 52 cikin 100, idan aka kwatanta da makonni biyu da suka gabata, a cewar jaridar New York Times.(Ibrahim)

Ibrahim