logo

HAUSA

Biden: saurin tabarbarewar halin da ake ciki a Afghanistan ya wuce zaton Amurka

2021-08-17 14:11:42 CRI

Shugaban kasar Amurka Joseph Robinette Biden ya ce, kudurin janye sojojin Amurka daga kasar Afghanistan ya dace, amma saurin tabarbarewar halin da ake ciki a kasar ya wuce zaton Amurka.

Bayan dawowar Biden fadar gwamnatin kasar wato White House daga sansanin hutu na Camp David a wannan rana jiya, ya yi jawabi kan halin da ake ciki a Afghanistan, inda ya sake nanata cewa, rundunar sojan Amurka ta kammala aikin yaki da ta’addanci a Afghanistan. Kana ci gaba da jibge rundunar a Afghanistan ba zai dace da muradun Amurka ba. Ba abin da zai yi sai dai janye sojojin, saboda gwamnatin Donald Trump ta daddale yarjejeniyar janye sojoji da kungiyar Taliban a bara.

Haka kuma Biden ya ce, saurin tabarbarewar halin da ake ciki a Afghanistan ya wuce zaton Amurka. Dalilin da ya sa haka shi ne domin shugaban Afghanistan ya bar kasarsa, sa’an nan rundunar Afghanistan sun mika wuya. Sauye-sauyen da aka samu a makon da ya gabata sun nuna cewa, kudurin janye sojojin Amurka daga Afghanistan ya dace. Kuma sojojin Amurka ba za su shiga wani yakin basasa, wanda al’ummar Afghanistan ma ba sa so su yi ba.

Har ila yau Biden ya nuna cewa, Amurka ta yi kuskure da dama a shekaru 20 da suka wuce a Afghanistan. Ana fama da matsaloli da dama wajen janye sojojin Amurka a wannan karo. Kuma kudurinsa zai sha suka, amma yana fatan sa ayar yakin Afghanistan, ba ya so mika alhakin kawo karshen wannan yaki zuwa ga shugaba na nan gaba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan