logo

HAUSA

Tilas Ne Amurka Da Ta Boye Bayanai Ta Amsa Tambayoyin Al’ummomin Duniya

2021-09-04 20:20:03 CRI

Bayan kwanaki sama da 90, ba a fito da wani sakamako cikin rahoton binciken asalin kwayar cutar COVID-19 ba, wanda hukumar leken asirin kasar Amurka ta kirkiro. Amma Amurka ta dora wa kasar Sin laifi, wai kasar Sin ta ki yarda ta samar da bayanai ga duniya. Hakika dai Abun da ta yi ya tono yadda ta boye bayanai masu ruwa da tsaki.

Aikin binciken asalin kwayar cutar, aiki ne na kimiyya. Muhimmin aiki a mataki na gaba shi ne gudanar da binciken a sassa daban daban na duniya. Ya kamata sassa masu ruwa da tsaki su taimaka. Amma abun da ake shakka shi ne, a matsayinta na kasar da ta fi samun masu kamuwa da cutar COVID-19 da matattu sanadiyyar cutar a duniya, Amurka ta ki yarda da bayyana wa jama’a bayanan da suka shafi wadanda suka kamu da cutar a farkon lokacin barkewarta, kana kuma ta kawo cikas wajen gano asalin kwayar cutar a cikin gidanta. Lamarin ya nuna cewa, Amurka ta boye wasu bayanai.

Yanzu al’ummomin kasa da kasa suna tambayar cewa, yaushe ne Amurka za ta bayyana wa jama’a bayanai masu ruwa da tsaki? Yaushe ne za ta gayyaci WHO ta gudanar da binciken asalin kwayar cutar a kasar? Yaushe ne za ta bude kofar sansanin Fort Detrick da dakin gwaje-gwajen jami’ar North Carolina don tawagar kasa da kasa ta yi bincike a cikinsu? Yaushe ne za ta koma kan hanyar gudanar da binciken kimiyya a maimakon siyasantar da aikin? Tilas ne Amurka ta ba da amsa. Idan ta ci gaba da kau da kai, to za ta zama kasa mafi gazawa wajen yaki da annobar a duniya, haka kuma kasar da cutar ta samo asali. Kasa da kasa na da hakkin kara sanin gaskiya, dangane da abun da ya shafi lafiya da rayukansu. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan