Lokaci Ya Yi Da Amurka Ta Kawo Karshen Hayaniyar Siyasa Kan Gano Asalin Kwayar Cutar COVID-19
2021-09-01 21:15:24 CRI
Kwanan baya, hukumar leken asirin kasar Amurka ta kaddamar da takaitaccen bayani kan rahoton bincike, bayan da ta shafe watanni 3 tana kokarin gano asalin kwayar cutar COVID-19.
A cikin wannan takaitaccen bayani, Amurka ta sha yin amfani da kalaman “watakila” da kuma “mai yiwuwa”. Ga alama ba ta ce kome ba cikin takaitaccen bayaninta. Amma hukumar leken asirin Amurka da fadar shugaban kasar wato White House sun yi dabara sosai, inda suka ci gaba da shafa wa kasar Sin bakin fenti, kana kafin su gudanar da bincike kan gano asalin kwayar cutar, sun riga sun yanke shawarar dora kasar Sin laifi.
Ba shakka an kaddamar da wannan rahoto ne sakamakon siyasantar da aikin gano asalin kwayar cutar, a maimakon amfani a tsari na kimiyya, wanda ba za a iya gaskatawa ba. Tun farkon kirkiro rahoton, hayaniyar siyasa ce kawai.
Tun tuni kasashen duniya sun fahimci cewa, wasu ‘yan siyasan Amurka ba su da niyya da kwarewa wajen gano asalin kwayar cutar. Dalilin da ya sa suka siyasantar da aikin gano asalin kwayar cutar shi ne, domin kin sauke nauyi dake wuyansu, da boye abubuwan da ake shakka a fannin yaki da annobar, a yunkurin shafa wa kasar Sin kashin kaji da hana ci gaban kasar Sin. Abubuwan da suke yi baki daya, makarkashiya ce. Yanzu Amurkawa sun la’anci gwamnatin Amurka wadda ta gaza wajen yaki da annobar. Sa’an nan kuma, hauhawar farashin kaya, janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan, takarar da ke tsakanin jam’iyyu 2 na Amurka, da dai sauransu sun matsa wa ‘yan siyasan Amurka lamba sosai, don haka, suka yi yunkurin dora wa wasu laifi don boye kuskurensu, inda suka sake zabar kasar Sin. Siyasantar aikin gano asalin kwayar cutar ta kasance wata hanyar da Amurka take bi wajen hana ci gaban kasar Sin. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Kasar Sin Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Kiyashin Da Amurka Ta Yi Wa ‘Yan Afghanistan
- Abun Da Amurka Take Yi, Mumuman Cikas Ne Ga Yaki Da Annoba Da Gano Asalin Kwayar Cuta A Duniya
- Sin: Ficewar Amurka A Afghanistan Ya Bude Wani Sabon Babi A Kasar
- Shin Sojojin Amurka Da Suka Kashe Mutane a Kabul Jarumai Ne?