logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin cimma burikan cikar rundunar PLA shekaru 100

2021-07-31 16:19:38 CMG

Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin cimma burikan cikar rundunar PLA shekaru 100_fororder_0731-Xi-PLA-Faeza-jpg

Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta ksar Sin (JKS) Xi Jinping, ya yi kira da a jajirce tare da aiki tukuru ta hanyar kan-kan da kai, don cimma burikan cikar rundunar ‘yantar da al’ummar Sinawa ta PLA shekaru 100 da kafuwa.

Xi Jinping wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin aikin soja na tsakiyar kasar, ya bayyana haka ne jiya Juma’a, yayin wani taron nazari na ofisin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS. (Fa’iza Mustapha)

Faeza