logo

HAUSA

Xi ya aike da sakon ta’aziyya dangane da mutuwar tsohon shugaban IOC

2021-08-31 20:18:17 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa shugaban kwamitin kula da wasannin Olympic na kasa da kasa IOC Thomas Bach, sakon ta’aziyya a ranar Litinin dangane da mutuwar tsohon shugaban kwamitin na IOC Jacques Rogge.

A cikin sakon nasa, Xi ya bayyana Rogge a matsayin shugaban IOC da ya yi fice, inda ya himmantu wajen bunkasa harka da ruhin Olympic, ya kuma cimma manyan nasarori wajen bunkasa harkar, musamman wasannin matasa.

Xi ya yi nuni da cewa, Rogge ya dade yana nuna kulawa tare da goyon bayan raya wasanni da harkar Olympic a kasar Sin, ya kuma bayar da muhimmiyar gudummowa wajen shirya gasar wasannin Olympic na shekarar 2008 da aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin cikin nasara. (Ibrahim)

Ibrahim