logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Kiyashin Da Amurka Ta Yi Wa ‘Yan Afghanistan

2021-09-01 20:38:13 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, duk da cewa Amurka ta fice daga cikin kasar Afghanistan, wajibi ne a bincike kisan kiyashin da sojojin Amurka da kawayenta suka aikata a kasar cikin shekaru 20 da suka gabata, a kuma hukunta wadanda ke da hannu.

Wang ya bayyana haka ne a Larabar nan, yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa, kan kisan fararen hula na baya-bayan nan da sojojin na Amurka suka aikata, lokacin da suke kokarin ficewa daga Afghanistan.

Rahotanni na cewa, a ranar 26 ga watan Agusta, wani harin ta’addanci da aka kai a kusa da filin jirgin saman Kabul, ya haddasa kisa da jikkata daruruwan jama’a. Wasu da suka jikkata, sun yi ikirarin cewa, sojojin Amurka sun yi harbi kan jama’a, bayan aukuwar fashewar, lamarin da ya haddasa jikkatar karin mutane.

Wang ya bayyana cewa, alkaluma sun nuna cewa, ya zuwa watan Afrilun shekarar 2020, a kalla fararen hulan Afghanistan 47,245 aka kashe a yakin da Amurka ta kaddamar a kasar Afghanistan. Yana mai jaddada cewa, ko da yake sojojin Amurka sun fice daga kasar Afghanistan, amma wajibi ne a gudanar da cikakken bincike, kan yadda ta yi wa fararen hula kisan kiyashi. Ya ce, ya kamata a kiyaye rayuka da hakkin bil-Adama na jama’ar Afghanistan. Wannan batu ne da ya shafi dokar kasa da kasa, da adalci, da ci gaban ‘yancin bil-Adama.(Ibrahim)

Ibrahim