Abun Da Amurka Take Yi, Mumuman Cikas Ne Ga Yaki Da Annoba Da Gano Asalin Kwayar Cuta A Duniya
2021-08-31 21:21:45 CRI
Kwanan baya, hukumar leken asirin kasar Amurka ta fitar da wani rahoton bincike dangane da gano asalin kwayar cutar COVID-19, inda aka bata sunan kasar Sin da laifin kawo cikas kan ayyukan bincike a duniya, kana an bukaci kasashen duniya da su matsa wa kasar Sin lamba ta fuskar siyasa. Irin wannan abun da Amurka ta yi ba tare da jin kunya ba, ya lalata hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar da kuma aikin gano asalin kwayar cutar.
A matsayinta na kasar da ta zama ta farko a duniya a fannonin gazawa wajen yaki da annobar da kuma baza kwayar cutar, me ya sa Amurka ta wakilci kasashen duniya? Kwanan baya, kasashe fiye da 80 sun aika wa babban dakataren WHO wasika, da ba da sanarwa ko kuma yin ganawa, inda suka nuna kin amincewa da siyasantar batun gano asalin kwayar cutar, sun kuma bukaci a tabbatar da sakamakon aikin gano asalin kwayar cutar na farko da aka gudanar. Sa’an nan kuma jam’iyyu, hukumomi, da dandalin kwararru fiye da 300 daga kasashe da yankuna sama da 100 sun mika wa sakatariyar WHO sanarwar hadin gwiwa ta kin amincewa da siyasantar da aikin gano asalin kwayar cutar ta COVID-19. Hakika hakan shi ne ra’ayi daya da kasashen duniya suka cimma.
Hakika yadda gwamnatin Amurka ta umurci hukumar leken asirinta gano asalin kwayar cutar, hayaniyar siyasa ce kawai. Ta kirkiro rahoton ne domin dora wa wasu laifi. Amurka ta fi samun masu kamuwa da cutar COVID-19 da kuma wadanda cutar ke halakawa a duniya, haka kuma ta fi baza kwayar cutar a duniya. Amurka ta kawo cikas sosai a duniya ta hanyoyin gazawa wajen yaki da annobar a cikin gida da kuma barin Amurkawa su yi tafiye-tafiye zuwa ketare yayin da yaduwar annobar ta yi tsanani. Sakamakon saurin karuwar masu kamuwa da cutar, ya sa kasashe mambobin kungiyar EU sanya Amurka cikin jerin kasashen da aka haramtawa matafiyansu.
Ga alama, kasashen duniya, ciki had da kawayen Amurka, sun fahimci cewa, yayin da sabbin nau’o’in kwayar cutar COVID-19 suke yaduwa, ‘yan siyasan Amurka sun ci gaba da baza kwayar cutar siyasa, lamarin da ya lalata kokarin kasashen duniya wajen yaki da annobar, tare kuma da sanya rayukan al’ummun kasa da kasa cikin hadari.
Shaidu sun tabbatar da cewa, Amurka, wadda ta siyasantar aikin gano asalin kwayar cutar, ta kasance mummunan cikas wajen yaki da annobar a duniya da kuma aikin binciken gano asalin kwayar cutar. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Tilas Ne A Yi Bincike Kan Dakunan Gwaje-Gwajen Amurka
- Rahoto wai na binciken asalin cutar COVID-19 na Amurka wauta ce da ta kara yi
- Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Sin: Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Ba Ta Hanyar Siyasantar Da Batun Gano Asalin Cutar COVID-19
- Kasar Sin Tana Goyon Bayan Aikin Binciken Gano Asalin COVID-19 Da WHO Ke Yi Amma Tana Adawa Da Yadda Ake Siyasantar Da Batun