logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya murnar cika shekaru 20 da ba da taimakon laimar kwadi ga kasashen waje

2021-09-02 14:40:59 cri

Yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murnar cika shekaru 20 da ba da taimakon laimar kwadi ga kasashen waje da kuma dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan samu ci gaba mai dorewa.

Xi Jinping ya taya murnar cika shekaru 20 da ba da taimakon laimar kwadi ga kasashen waje_fororder_CqgRLlvvYsOAeaESAAAAAAAAAAA814.640x425

A shekarar 2001 ne, aka kafa sansanin nuna fasahar laimar kwadi da kasar Sin ta ba da taimako ga kasashen waje na farko a kasar Papua New Guinea. Ya zuwa yanzu, an inganta wannan fasaha zuwa kasashe fiye da 100. An gudanar da irin wannan hadin kai ne da nufin kawar da talauci, karfafa samar da guraban aikin yi, amfani da albarkatun da ake sabuntawa, da kuma tinkarar sauyin yanayi da dai sauransu, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta bunkasuwa da zaman rayuwar jama’ar wurin, shirin ya samu karbuwa sosai a kasashe masu tasowa.

Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa, don ci gaba da ba da gudummawar hikimarta da shirinta na aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030, ta yadda fasahar laimar kwadi za ta iya kara amfanawa jama’ar kasashe masu tasowa. (Bilkisu Xin)