logo

HAUSA

Sin: An Bude Sabon Babi A Tarihin Afghanistan

2021-09-01 19:33:42 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Laraba cewa, an bude wani sabon babi a tarihin kasar Afghanistan, yayin da kasar da yaki ya daidaita, ta kama turbar tabbatar da zaman lafiya da sake gina kasar.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa ya ce, kasar Sin tana fatan bangarorin da abin da ya shafa a kasar Afghanistan, za su kafa tsarin siyasa mai salon bude kofa da zai kunshi dukkan sassa, su kuma bijiro da matsakaitan manufofi na cikin gida da na ketare masu dorewa, kana su katse duk wata hulda baki daya da dukkan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Kalaman Wang Wenbin na zuwa ne, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game a rahotanni dake cewa, kungiyar Taliban za ta sanar da kafa sabuwar gwamnati a ranar Jumma’a. (Ibrahim)

Ibrahim