logo

HAUSA

Sin: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Zuba Jari Zai Samu Makoma Mai Kyau

2021-08-30 21:12:05 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin tana karfafawa kamfanoninta gwiwa, da su martaba matakan raya nahiyar Afirka, su kuma ba da gudummawa ga ‘yancin kasashen nahiyar na samun ci gaba mai dorewa.

Wang Wenbin ya bayyana haka ne, a yayin taron manema labaran da aka shirya Litinin din nan, game da rahoto kan jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a Afirka, inda jama’a daga bangarori daban-daban na rayuwa suka yi bayani sosai a kai. An yi imanin cewa, jarin da kamfanomin kasar Sin suka zuba a nahiyar Afirka, ya taimakawa sassan biyu, ya kuma biya bukatun raya nahiyar yadda ya kamata. Kana hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin zuba jari na da kyakkyawar makoma.

Wang ya kara da cewa, har kullum gwamnatin kasar Sin, tana karfafawa kamfanoninta gwiwa, da su rika cundaya da al’ummomin Afirka, su kuma sauke nauyin dake bisa wuyansu a fannin zamantakewa, su taimakawa mazauna wurin, su ba da gudummawa ga ‘yancin kasashen nahiyar Afirka, na samun ci gaba mai dorewa. (Ibrahim)

Ibrahim