logo

HAUSA

Sin: Ficewar Amurka A Afghanistan Ya Bude Wani Sabon Babi A Kasar

2021-08-31 20:13:17 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana Talatar nan cewa, an bude wani sabon babi a tarihin kasar Afghanistan, bayan janyewar dakarun kasar Amurka daga cikin kasar da yaki ya daidaita.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, ficewar Amurka daga kasar ta Afghanista, ya nuna cewa, manufar shiga tsakani ta hanyar soja da kakaba dabi’u da tsarin zamantakewa kan wasu kasashe, ba ta taba yin nasara ba. Yana mai cewa, abubuwan da suka faru a tarihin kasar Afghanistan da shaidu a zahiri sun nuna cewa, idan har ana fatan samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki, akwai bukatar kasar Afghanistan ta gina tsarin siyasa mai salon bude kofa da zai kunshi dukkan sassa, ta kuma bi matsakaitan manufofin cikin gida da na ketare masu dorewa, da katse duk wata hulda da kungiyoyin ‘yan ta’adda kwata-kwata.

Wang ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tattaunawa da dukkan sassa dake kasar Afghanistan da ma ragowar kasashen duniya, za ta kuma samar da goyon baya da taimako ga Afghanistan gwargwadon karfinta, don ganin an maido da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki, da yakar dukkan kungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki har da kungiyar Islama ta gabashin Turkestan (ETIM) a Afghanistan.(Ibrahim)

Ibrahim