Xi ya jaddada bukatar yaki da babakere, gurbata muhalli da inganta tsarin ajiyan ketare na kasar
2021-08-30 20:33:33 CRI
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar kare kaimi, wajen karfafa yaki da tsari na babakere da yin takara na rashin adalci, da inganta tsarin ajiyar kudaden kasar na ketare, a kuma yi yaki da gurbata muhalli.
Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kwamitin kolin aikin soja, ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke jagorantar taron kwamitin koli kan zurfafa yin gyare-gyare daga dukkan fannoni karo na 21. (Ibrahim)