logo

HAUSA

Shugaba Xi ya jaddada manufar kara azama wajen sauya tsarin amfani da ban daki a yankunan karkara

2021-07-23 19:55:30 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada manufar kara azama wajen sauya tsarin amfani da ban daki a yankunan karkarar kasar Sin, yana mai kira da a kara azama, wajen aiwatar da dukkanin matakai na tabbatar da inganci, da sakamako mai gamsarwa a fannin yayata wannan manufa.

Shugaba Xi ya jinjinawa kwazon da aka yi a shekarun baya bayan nan, wanda hakan ya haifar da ci gaba a fannin inganta tsaftar muhalli a yankunan karkara. Ya ce sauyi a tsarin amfani da ban dakuna a karkara, zai ci gaba da zama muhimmin aiki, na farfado da yankunan cikin shekaru 5 masu zuwa.

Daga nan sai ya kara kira da a kara karfafa ayyukan da ake yi a wannan fanni, daidai da yanayin yankunan na karkara bisa matakan kimiyya, tare da kaucewa tsawaita matakan gudanarwa da barnata kudade.

An dai karanta umarnin na shugaba Xi, a yayin taron kasa game da sauyi kan yadda ake amfani da ban dakuna a yankunan karkara, taron da ya gudana a Juma’ar nan a birnin Hengyang, na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.  (Saminu)

Saminu