logo

HAUSA

Tilas Ne A Yi Bincike Kan Dakunan Gwaje-Gwajen Amurka

2021-08-29 21:15:01 CRI

Kwanan baya, hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta gabatar da wani rahoton bincike dangane da batun gano asalin kwayar cutar COVID-19, inda ta ce, ba za a iya kawar da yiwuwar bullar kwayar cutar daga dakin gwaje-gwaje ba. Kasar Sin tana goyon bayan gano asalin kwayar cutar ta hanyar kimiyya. A karshen watan Maris na bana ne tawagar kwararru ta hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya WHO da kasar Sin suka gabatar da wani rahoto, wanda ya nuna cewa, ba zai yiwu kwayar cutar ta COVID-19 ta bulla daga dakin gwajin kasar Sin ba. Amma Amurka ta dage kan cewa, zai yiwu kwayar cutar ta bulla daga dakin gwaji, to, kamata ya yi ta yi adalci, ta bude dakunan gwaje-gwajenta, don a yi musu bincike kamar yadda aka yi a kasar Sin.

Yanzu masanan kimiyya na kasa da kasa suna ganin cewa, an kammala aikin gano asalin kwayar cutar COVID-19 a kasar Sin, sun kuma amince da yadda kasar Sin ta sauke nauyi bisa wuyanta da kuma tafiyar da harkoki masu ruwa da tsaki a fili ba tare da rufa-rufa ba. Kowa yana sane da cewa, cibiyar nazarin kwayoyin cutuka ta Wuhan ta karbi masanan WHO har sau biyu, yayin da ya zuwa yanzu Amurka ba ta bude dakunan gwaje-gwajenta ba tukuna, musamman ma dakunan gwaje-gwajen Fort Detrick da jami’ar North Carolina, wadanda suka dade suna nazarin kwayar cuar coronavirus, sun kuma gaza wajen tabbatar da tsaro, lamarin da ya haifar da shakku mai yawa a kasashen duniya. Amurka ta ce, ba a iya kawar da yiwuwar bullar kwayar cutar daga dakin gwaji ba, to, dole ne ta bude kofar wadannan wurare biyu don a yi musu bincike.

Yayin da kasashen duniya suka yi ta yin kiran a yi bincike kan dakunan gwaje-gwajen Amurka, idan Amurka ba ta amsa kiran ba, ta ki a yi mata bincike, to, za a kara fahimtar ainihin nufinta na siyasantar da batun gano asalin kwayar cutar COVID-19, da kuma kasancewarta a matsayin kasar da aka samu asalin kwayar cutar. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan