logo

HAUSA

Shin Sojojin Amurka Da Suka Kashe Mutane a Kabul Jarumai Ne?

2021-08-30 20:01:49 CRI

A daren ranar 26 ga wata, daruruwan mutane sun rasa rayukansu da jikkata a wasu hare-hare 2 da aka kai a kusa da filin jirgin saman Kabul da ke kasar Afghanistan. Bayanan da wadanda suka jikkata cikin hare-haren suka yi, sun tono gaskiyar abubuwan da suka faru, wato sojojin kasar Amurka da suka janye jikinsu daga Afghanistan cikin tsoro, sun kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba a filin jirgin saman. A maimakon ‘yan ta’adda, fararen hular Afghanistan din sun gamu da ajalinsu ne sakamakon harbe-harben da sojojin Amurka suka yi, wadanda da ma suka zo Afghanistan ne da sunan “ceton rayukan ‘yan Afghanistan”.

Duk da haka, cikin jawabinsa biyo bayan abkuwar hare-haren, shugaban Amurka Joe Biden ya ayyana sojojin Amurka da suka rasa rayukansu a filin jirgin saman a matsayin jarumai, ya kuma yi alkawarin daukar fansa, amma bai ambato fararen hular Afghanistan da suka mutu a filin jirgin saman ba. A ganinsa, irin wannan abun tausayi bai taba abkuwa ba.

Gaskiyar magana shi ne, sojojin Amurka sun kutsa kai cikin Afghanistan, kana kuma Amurka ce ta haddasa rudanin dake faruwa a Afghanistan. Ko da yake Amurka ta mayar da fari baki kan yakin da ta tayar a Afghanistan, tare da ayyana sojojinta da suka kashe wadanda ba su ji ba, ba su gani ba a matsayin jarumai, amma ba za ta iya boye yadda ta haifar da bala’in jin kai a Afghanistan ba. Sa’an nan kuma za a fahimci yadda Amurka ta nuna fuska biyu kan batun kiyaye hakkin dan Adam. Lalle mai rajin kare hakkokin bil Adama shi ne ya ke keta hakkokin bil Adama.(Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan