logo

HAUSA

Ta yaya JKS ta samu ci gaban al’ajabi da ba a taba ganin irinsa ba”

2021-08-27 21:57:02 cri

Ta yaya JKS ta samu ci gaban al’ajabi da ba a taba ganin irinsa ba”_fororder_1

“Kasar Sin ta samu ci gaban al’ajabi da ba a taba ganin irinsa ba ... A hakika, za a iya danganta wadannan nasarori da abu daya, wato shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.” A kwanakin baya, Sheriff Ghali Ibrahim, daraktan sashin kula da huldar kasa da kasa na jami'ar Abuja dake Najeriya, ya wallafa wata kasida a kafafen yada labarai, inda ya bayyana ra'ayinsa kan nasarorin da kasar Sin ta samu na ci gaba. Akwai manazarta da dama a kasashen duniya, wadanda ke da ra'ayi daya da Sheriff. Abin da suke son kara fahimta shi ne: Ta yaya JKS ta jagoranci jama’ar kasarsu wajen samun wadannan ci gaba na al’ajabi? Wata muhimmiyar takarda ta baya-bayan nan da Sashen Yada Labarai na Kwamitin Tsakiya na JKS ya wallafa mai taken “Nauyin da JKS ta dauka da kuma gudummawar da ta bayar” ya ba da cikakkiyar amsa kan wannan tambaya.

Babban dalilin da ya sa kasar Sin ta samu gagarumar nasara, shi ne yadda JKS ta tsaya tsayin daka wajen jagorantar jama’ar kasar ta hanyar da ta dace da yanayin kasar. Bayan Yakin Duniya na Biyu, ana ganin tsarin yammacin duniya shi ne kawai na iya zamanantar da kasa. Amma, kasashe masu tasowa da yawa wadanda ke bin tsarin yammacin duniya sun gano, tsarin bai dace da su ba.

A nata bangare, JKS ta nace ga 'yancin kai kuma tana jagorantar jama’ar kasar don nemo hanyar gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin. A sa’i daya kuma, sun gudanar da jerin sabbin bincike, wadanda suka inganta karfin samar da kayayyaki. Musamman ma an dauki matakan yin kwaskwarima fiye da 2400 tun bayan babban taron wakilan kasa karo na 18 na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wandanda suka kawar da abubuwan da ke haifar da cikas ga hanawa da takaita ci gaba, ta yadda aka karfafa karfin bunkasuwa. 

A cikin ‘yan shekarun nan, bisa halin da kasashen duniya ke ciki na fuskantar yanayi na rashin tabbas, JKS ta tsaida kudurin mayar da hankali kan raya tattalin arziki a cikin gida tare da hade kasuwar cikin gida da ta ketare, domin samun ci gaba mai karfi da dorewa, hakan ya kara karfi na samun ci gaba mai inganci. Kamar yadda tsohon sakataren ofishin siyasa na jam’iyyar kwaminis ta kasar Isra’ila ya fada, “Bai kamata a kira manyan sauye-sauyen da ake yi a kasar Sin abin al’ajabi ba, saboda ana kiran abubuwan da ake ganin ba za su yiwu ba, a matsayin al’ajabi, sauye-sauyen dake faruwa a kasar Sin gaskiya ne, ya kamata a kira su abubuwa na kimiyya.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)