logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da bayani mai taken “Ruhin JKS ya zama arzikin jam’iyyar da ta kasar Sin”

2021-08-31 16:34:21 CRI

Gobe 1 ga watan Satumba, mujallar neman gaskiya wato Qiushi a Sinanci za ta wallafa bayanin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai taken “Muhimmin ruhin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS ya zama arziki ne ga jam’iyyar da kasar Sin ”.

Bayanin ya jaddada cewa, wata al’umma ba za ta iya samun bunkasuwa ba idan ba ta da ruhi mai inganci. Jam’iyyar JKS dake samun bunkasuwa mai kyau ba tare da katsewa ba a cikin shekaru dari da suka gabata, tana da nagartar ruhi mai inganci, wanda ke taimakawa wajen magance wahalhalu da bunkasa tattalin arziki har ma da inganta tunanin jama’a. (Amina Xu)