Xi ya jadadda bukatar inganta ayyukan JKS da suka shafi kabilu
2021-08-28 21:06:14 CRI
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar karfafa hadin kan al’ummar Sinawa da kuma daukar dabarun da suka dace da sigar kasar Sin, wajen tafiyar da harkokin da suka shafi kabilu.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin babban taro kan harkokin da suka shafi kabilu daban-daban na kasar.
Ya ce dole ne a sabon zamanin da ake ciki, karfafa hadin kan al’umma ya kasance kan gaba cikin ayyukan JKS da suka shafi kabilu, yana mai cewa dole ne a daukaka daidaitacciyar mahangar tarihin kasar Sin, kana a bunkasa asali da alfahari da kasa.
Ya kara da cewa, wajibi ne a tabbatar da daidaito tsakanin dukkan kabilu, kana a tabbatar da riko da tutar hadin kan kasar. (Fa’iza Mustapha)