logo

HAUSA

IPC ta karrama tsohon shugaban IOC Rogge

2021-08-30 14:32:43 CRI

IPC ta karrama tsohon shugaban IOC Rogge_fororder_210830-Ahmad 3-Rogge

Kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta nakasassu na kasa da kasa IPC, a yau Litinin ya girmama tsohon shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic ta kasa da kasa (IOC) Jacques Rogge wanda ya rasu a ranar Lahadi.

Rogge shi ne shugaban kwamitin IOC na takwas wanda ya shugabance ta tsakanin shekarar 2001 zuwa 2013. Ya mutu a ranar Lahadi yana da shekaru 79.

A sanarwar da shugaban IPC, Andrew Parsons, ya fitar ya bayyana cewa, a koda yaushe Jacques ya nuna goyon bayansa ga wasannin motsa jiki na nakasassu kuma za a jima ana tuna shi a wannan fannin ga dukkan wadanda suka san shi.

A lokacin da yake shugabantar kwamitin na IOC, ya sanya hannu kan yarjejeniyoyi masu yawa wadanda ba kawai sun daidaita kwamitin IPC ba ne har ma sun taimakawa kungiyar wajen samun bunkasuwa da farin jini.

A shekarar 2017, an nuna gamsuwa da yabo ga irin gwagwarmayar da ya yi ga tsarin wasanninn motsa jiki na nakasassu. Don haka a Tokyo, an karrama shi ta hanyar sauko da tutoci kasa kasa a filin wasannin. (Ahmad Fagam)