logo

HAUSA

Bach ya ba da shawarar kara kalmar "tare" a taken gasar Olympics bayan sake zaben sa shugaban IOC

2021-03-11 11:06:38 CRI

Shugaban kwamitin kasa da kasa mai shirya gasar Olympic Mr. Thomas Bach, ya ba da shawarar kara kalmar "tare" cikin taken gasar Olympic, bayan sake zabar sa shugaban kwamitin na IOC.

Thomas Bach, ya ce baya ga kalmomin "Sauri, da daukaka, da karfi", kamata ya yi a kara kalmar “Tare” cikin kalmomin dake nuni ga manufar shirya gasar ta Olympic. Mr. Bach ya furta wannan shawara ne, bayan da aka sake zabar sa a matsayin jagoran kwamitin IOC, yayin taron kwamitin na 137 da ya gudana ta kafar bidiyo, wanda kuma aka shirya a jiya Laraba daga birnin Lausanne na kasar Switzerland.

Kasancewar sa dan takara daya tilo da ya tsaya zaben shugabancin kwamitin na IOC, Bach ya lashe kuri’u 93 cikin 94 da mambobin kwamitin na IOC suka kada ta yanar gizo. Da kuma wannan sakamako, Bach zai jagoranci kwamitin har zuwa shekarar 2025.

A wani ci gaban kuma, babban jami’in na IOC ya bayyana karfin gwiwar sa, game da shirin kwamitin tsara gasar Olympic ta lokacin hunturu da za a yi badi a birnin Beijing na kasar Sin, yana mai cewa, za a shirya kasaitacciyar gasa mai ban sha’awa.

Ya ce an kammala daukacin filayen wasa. Kuma ba da jimawa ba, aka gudanar da gwajin amfani da sassan tsaunukan da za a gudanar da wasu wasanni cikin su. Duk da kuma kalubalen barkewar cutar COVID-19, ana iya ganin yadda kwamitin shirya gasar na birnin Beijing ya shirya tsaf. Ko shakka babu, kwamitin ya gama shiryawa gabatarwa duniya gasar lokacin hunturu mafi kayatarwa.  (Saminu)

Saminu