logo

HAUSA

Shugaban kwamitin IOC ya taya shugaba Xi murnar bikin bazara

2021-02-12 20:26:52 CRI

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics ta duniya Thomas Bach, ya aike da wata wasika mai dauke da gaisuwar sabuwar shekara ga shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Cikin wasikar, Thomas Bach ya yi wa shugaba Xi da al’ummar Sinawa fatan kasancewa cikin koshin lafiya da wadata da ci gaba, a sabuwar shekarar Saniya.

A cewarsa, shekarar ta Saniya na da muhimmanci ga wasannin Olympics, yana mai cewa albarkacin wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing dake karatowa, duniya za ta hadu karkashin inuwa guda ta zaman lafiya da ci gaba da kuma abota.

Thomas Bach, wanda ya bayyana kwarin gwiwarsa kan kasar Sin, ya ce kasar ta shirya tsaf domin gudanar da wasannin. Ya ce burin shugaba Xi na shigar da Sinawa miliyan 300 cikin wasannin lokacin hunturu ya kusa tabbata, yana mai yi wa ‘yan wasan kasar Sin fatan samun nasara.

Har ila yau, ya ce yana da yakinin karkashin shugabancin Xi Jinping, Sin za ta ci gaba da samun gagagrumar nasara a shekarar Saniya. (Fa’iza Mustapha)