logo

HAUSA

Sin ta shirya karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin hunturun 2022 in ji wani mamban IOC

2021-06-10 13:26:08 CRI

Sin ta shirya karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin hunturun 2022 in ji wani mamban IOC_fororder_src=http___s9.rr.itc.cn_r_wapChange_201610_27_12_a2f95c3466228251074.jpeg&refer=http___s9.rr.itc

Mambar kwamitin shirya gasar Olympic ta kasa da kasa IOC, kuma mamba a hukumar zartaswa ta shirya gasar Olympic a kasar Thailand Patama Leesawattrakul, ta ce Sin ta shirya tsaf, domin karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin hunturun 2022.

Uwargida Patama, wadda ke wannan tsokaci yayin zantawar ta a baya bayan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ta ce "Irin kwarewar da Sin ta samu daga shirya gasar Olympics ta lokacin zafin shekarar 2008, zai yi amfani yayin gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturun 2022, kuma birnin Beijing zai kasance birni na farko da zai karbi bakuncin gasar Olympics har karo biyu, wato ta lokacin zafi da kuma hunturu.

Jami’ar ta kara da cewa, Sin ta yi matukar kokari wajen shirya wannan gasa ta 2022 dake tafe, inda tuni ta gina filaye da gyara wasu masu yawan gaske, ya zuwa karshen shekarar 2020, ta kuma cimma dukkanin nasara.

Patama, wadda kuma ita ce ke jagorantar hukumar raya al’adu ta kwamitin IOC, ta kuma jaddada kwazo kasar Sin a fannin tabbatar da shiri mai kunshe da dabarun kare muhalli, da aiki tare, ba tare da rufa rufa ba.

Ta ce "Na jinjinawa kokarin kasar Sin na karbar bakuncin gasar ta badi, karkashin manufar kare albarkatu, da kare muhalli, da daidaita muhallin halittu. Amfani da makamashi mai tsafta a dukkanin wuraren gudanar gasar na kara nuna himmar kasar Sin, wajen tabbatar da nasarar gudanar hakan cikin nasara.

Ta ce Sin ta yi gaba, wajen shawo kan annobar COVID-19, da farfadowar tattalin arziki. Duk da koma baya da bullar COVID-19 ta haifar, kana hukumar shirya gasar ta birnin Beijing ta ci gaba da kimtsawa, da aikin tsarawa da shirya komai yadda ya kamata, ta kuma kafa kwamitin ko ta kwana na dakile sake bullar COVID-19. Wannan ya kara nuna kwazon kasar Sin, da karfin gwiwar ta na tabbatar da cimma nasarar karbar bakuncin gasar yadda ya kamata.

Mrs. Patama ta ce, a matsayin kasarta, ta kasa dake yanki mai zafin yanayi, Thailand ba ta da yanayi na yau da kullum, na gudanar da wasannin gasar kankara, amma duk da haka, wasan na samun karin tagomashi cikin gwamman shekarun baya bayan nan.

Ta raka da cewa, a yayin gasar Olympics ta lokacin hunturun shekarar 2022, ‘yan wasan motsa jiki na Thailand za su shiga a dama da su, a gasar kasa da kasa ta zamiyar kankara nau’in skiing, da Alpine skiing. Har ila yau ‘yan wasa daga Thailand za su iso kasar Sin, wata guda gabanin fara gasar, domin su saba da yanayin muhallin kasar ta Sin.

Ya zama wabiji a kara kyautata ka’idojin kasar CUBA ta Sin

A kwanakin nan, gasar kwallon kwando ta jami’oin kasar Sin ko CUBA a takaice, ta ja hankalin sassa daban daban, sakamakon wata doka da ta shafi wasannin dake karkashin wannan gasa da ta jawo kace-nace.

Za dai a jima ana tuna yadda wani wasa ya kare, tsakanin jami’ar Peking da China University of Mining and Technology, wanda kungiyoyin biyu suka buga a mataki na 4 na karshen gasar ta CUBA, a ranar 5 ga watan nan na Yuni.

Yayin wannan wasa dai, kungiyoyin biyu sun yi kunnen doki, lokacin da ya rage mintuna 20 a tashi wasan, wanda hakan ya sanya dan wasan kungiyar Peking ya watsar da damar zura kwallaye 2 a ragar abokan karawarsa, da nufin wasan ya shiga zangon karin lokaci.

Karkashin dokokin gasar CUBA, saka kwallayen biyu ba zai baiwa kungiyar Peking damar lashe wasan na kusa da kusan na karshe ba.

A wasa na farko na wasan kusa da kusan na karshe, kungiyar Peking ta yi rashin nasara da ci 83 da 78, tsakanin ta da kungiyar wasa ta jami’ar China University of Mining and Technology, wanda hakan ke nufn sai kungiyar ta Peking ta samu karin maki 6 a wasan zagaye na biyu, kafin ta samu buga wasa na gaba.

Don haka ‘yan wasan Peking suka shirya dabarar shigar da wasan zangon karin lokaci, don su samu damar zura karin kwallaye, wanda kuma hakan ya ba su damar lashe wasan da maki 10.

Masharhanta kan wasan sun ce abun da ‘yan wasan kungiyar Peking suka yi bai sabawa dokar gasar ba, wadda ta tanadi karin lokaci idan kungiyoyi biyu suka yi kunnen doki, a wasan neman gurbin buga wasan kusa da kusan na karshe, ta yadda bisa wannan tanadi kungiyar dake da yawan kwallaye, za ta samu damar buga wasa na gaba. Wato dai bayan yin kunnen doki, kungiyar da ta samu maki mafi yawa ce za ta kai ga wasa na gaba.

To sai dai a nan abun tambayar shi ne, shin dabarar da kungiyar Peking ta yi amfani da ita ta dace? Bayan kammalar wasan, wasu masu bibiyar wasan kwallon kwando na Sin, sun bibiyi dokar gasar tun daga 2019, inda suka tarar da babban sauyi a tanadin dokar da ta ake aiwatarwa a shekaru biyun baya bayan nan.

Bisa dokar 2019, kungiyar za ta cimma nasara ne kawai, ta hanyoyi biyu: ko dai ta lashe wasannin ta biyu, ko samun maki mafi yawa ta hanyar zura kwallaye, idan an zo wasa na biyu kuma aka yi kunnen doki.

To sai dai kuma a bana, an gudanar da wasu sauye sauye, inda aka tsara fitar da wanda ya yi nasara kafin zuwa wasa na gaba. Wannan ne ya sanya kungiyar Peking ta dauki matakain kaiwa ga karin lokaci, maimakon jefa kwallaye biyu gabanin tashi wasan.

A na ta bangaren, kungiyar wasa ta China University of Mining and Technology, ta yi iya kokarin samun karin maki cikin zangon wasan na farko. Da ace sun ba su yi asarar wasu maki ba cikin wasan, da su ne za su yi nasara karkashin dokar gasar ta yanzu. A daya hannun kuma, idan har aka ci gaba da salon da kungiyar Peking ta yi amfani da shi a wasannin gaba, to hakan na iya sanyawa ‘yan wasa su rika shiga buga kwallo da zuciya biyu, kamar dai yadda wani masharhanci kan wasan ya bayyana a shafin sada zumunta na “Weibo”.

Ita ma jaridar People's Daily sashen wasanni ta bayyana ra’ayin ta, tana mai cewa, ya dace salon gasar ya ingiza dukkanin kungiyoyi su yi kwazo wajen buga wasa, tare da nuna kwarewa yayin da ake taka leda. Jaridar ta ce wannan batu ne da ya kamata a yi zuzzurfar tattaunawa a kan sa.

Jaridar ta kara da cewa, gasar kwallon kwando ta jami’oi ta samu babban ci gaba, kuma masu sha’awar wasan na matukar karuwa a shekarun baya bayan nan, don haka wani lokacin akan samu takaddama kan wasu batutuwa masu nasaba da wasan. To amma fa a cewar jaridar, dole ne a fuskanci irin wadannan takaddama, a kuma lura da damuwar ‘yan wasa da abubuwan da ‘yan kallo ke fatan gani a tsarin gasa mai gamsarwa, ta yadda hakan zai zama hanyar ingiza ci gaban gasar a nan gaba.