logo

HAUSA

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Sin: Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Ba Ta Hanyar Siyasantar Da Batun Gano Asalin Cutar COVID-19

2021-08-28 21:28:04 cri

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Sin: Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Ba Ta Hanyar Siyasantar Da Batun Gano Asalin Cutar COVID-19_fororder_111

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu ya amsa gayyatar wata hira ta musamman da babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ya yi masa a yau Asabar, inda ya gabatar da jawabi kan rahoton binciken asalin cutar COVID-19 da hukumar leken asirin Amurka ta fitar.

Kwanan nan, hukumar leken asirin Amurka ta tattara rahoton bincike kan wai batun asalin cutar COVID-19. Wannan abin da ake kira rahoto, rahoton siyasa ne na karya, ba tare da bin shaidun kimiyya da samun amincewa ba. Amurka ta kuma fitar da wata sanarwa, inda ta yi batanci da sukar kasar Sin. Game da haka, kasar Sin ta riga ta nuna adawarta, kuma ta gabatar da bukatar shawarwari mai tsanani da Amurka.

Amurka ta zargi Sin da rashin tsare gaskiya da bada hadin kai kan batun binciken asalin cutar COVID-19, wannan karya ce tsagwaronta. Kasar Sin tana ba da muhimmanci da gudummawa sosai a cikin hadin gwiwar kasa da kasa kan ayyukan binciken asalin cutar COVID-19 ta hanyar kimiyya. Kuma bisa manufar bin kimiyya da tabbatar da gaskiya, ta gayyaci kwararrun WHO zuwa kasar har sau biyu don gudanar da nazarin gano asalin cutar. A farkon wannan shekarar, tawagar hadin gwiwa dake hade da kwararrun kasa da kasa da na kasar Sin, ta gudanar da bincike da nazari na kwanaki 28 a kasar Sin, kuma sun fitar da rahoton bincike na hadin gwiwa tsakanin Sin da WHO, wanda ya kai ga samun sakamakon dake da karfin fada a ji da tabbatar da kwarewa da kuma hujjoji na kimiyya. Ta hakan aka kafa wani tushe mai kyau na ayyukan hadin kan kasa da kasa game da binciken asalin cutar. Kullum muna goyon baya kuma za mu ci gaba da himmatuwa wajen shiga ayyukan binciken asalin cutar ta hanyar kimiyya, amma muna adawa da siyasantar da ayyukan.

Dangane da batun binciken asalin cutar, wadda ta yi rufa-rufa da kin daukar alhaki da bada hadin kai ita ce kasar Amurka. Har zuwa yanzu Amurka ta ki mayar da martani ga shakkun da gamayyar kasashen duniya suka yi game da cibiyar gwajin halittu ta Fort Detrick da sansanonin nazarin halittu sama da 200 da ta kafa a kasashen ketare, tana kokarin boye gaskiya da gujewa daukar alhaki. Ya kamata Amurka ta sauke alhakin dake kanta na ba da amsa ga kasa da kasa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)