logo

HAUSA

Rahoto wai na binciken asalin cutar COVID-19 na Amurka wauta ce da ta kara yi

2021-08-28 21:54:54 cri

Rahoto wai na binciken asalin cutar COVID-19 na Amurka wauta ce da ta kara yi_fororder_微信图片_20210828213105

Jiya Jumma’a, hukumar leken asirin kasar Amurka ta fitar da muhimman abubuwa dangane da abun da ta kira “Rahoton Binciken Asalin Cutar COVID-19”, inda ba a samu tabbacin sakamakon ba, amma ta dora laifin rashin samun sakamakon gano asalin cutar kan kasar Sin. Daga baya Fadar White House ta fitar da wata sanarwa da ke bata sunan kasar Sin na kin musayar bayanai da kuma kawo cikas ga aikin binciken kasa da kasa na gano asalin cutar.

Wannan wauta ce da Amurka ta kara yi na siyasantar da batun binciken asalin cutar. Wannan abin da ake kira rahoto bai dogara da shaidun kimiyya ba haka kuma ba shi da aminci. A hakika dai, tun lokacin da Fadar White House ta umarci hukumar leken asirin da ta jagoranci binciken asalin cutar fiye da watanni uku da suka gabata, ta kuma samar da “sakamako” a cikin gajeren lokaci, sai kasashen duniya suka gano cewa, makasudin Amurka shi ne amfani da batun gano asalin cutar don “dora laifi” kan kasar Sin.

Matakin Sin na dogaro da kimiyya da nuna kwarewa da sanin ya kamata dangane da bibiyar asalin kwayar cutar, abu ne dake bayyane ga duniya baki daya. Kungiyar kwararru ta kasa da kasa ta WHO ta ziyarci kasar Sin sau biyu don gudanar da ayyukan bincike na hadin gwiwa kan gano asalin cutar, inda suka gana da duk mutanen da suke son gani, tare da duba duk kayayyakin da suke son gani. Rahoton bincike na hadin gwiwa wanda WHO da Sin suka bayar sun yi imanin cewa, “bai zai yuwu” cutar COVID-19 ta fita daga dakin gwaji ba. Wannan kudurin ya sami goyon baya da amincewa daga masana kimiyya na duniya baki daya.

A zamanin yau, hukumar leken asirin Amurka da ke da kwarewa a fannin shirya karya ba ta iya samar da ainihin abun da 'yan siyasar kasar ke tsammani ba, wannan ya nuna cewa, duk wata manakisa ta siyasa, za ta sha kaye a gaban kimiyya, kuma sakamakon da aka samu bisa matakin farko na gano asalin cutar zai iya cin jarrabawa a fannonin kimiyya da tarihi. (Mai fassara” Bilkisu Xin)