logo

HAUSA

Kasar Sin Tana Goyon Bayan Aikin Binciken Gano Asalin COVID-19 Da WHO Ke Yi Amma Tana Adawa Da Yadda Ake Siyasantar Da Batun

2021-08-13 20:04:16 CRI

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu, ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin tana goyon baya tare da shiga a dama da ita a aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19, amma fa tana adawa da yadda ake siyasantar da aikin binciken. Ma ya bayyana haka ne, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, yayin wani taro da wakilai da jakadu daga kasashe 29 dake nan kasar Sin.

Ma ya yi karin haske kan wasu fannoni guda 4 dake bayyana matsayin kasar Sin, game da aikin binciken gano asalin kwayar cutar a duniya. Na farko, aikin binciken cutar, batu ne na kimiyya, don haka masana ne kadai za su gano asalin kwayar cutar, da yadda take yaduwa zuwa ga bil-Adama ta hanyar bincike. Na biyu, rahoton binciken cutar na hadin gwiwa tsakanin masanan kasar Sin da WHO, ya shata matsaya tare da ba da shawarwarin, wanda al’umma duniya da ma masana baki daya suka amince da shi, wanda kuma wajibi ne a mutunta shi, kana dukkan sassa su aiwatar da shi, ciki har da sakatariyar WHO. Na uku, har kullum kasar Sin tana goyon baya, kuma za ta ci gaba da shiga a dama da ita a aikin binciken bisa mataki na kimiyya. Na hudu, ya kamata kuma ya zama wajibi, aikin binciken gano asalin kwayar cuyar a duniya, ya kasance karkashin jagorancin kasashe mambobin WHO.

Ma ya kuma yi nuni da cewa, wasu kasashe kamar Amurka, ta yi watsi da shaidu, har tana zargin kasar Sin da kin amincewa a gudanar da aikin binciken gano asalin cutar, tare da kambama tunanin da wasu ke yi wai, cutar ta bulla ne daga dakin bincike. Yana mai cewa, Amurka tana son yin amfani da zato na aikata laifi, da binciken cin zali, don neman hukunta kasar, wanda hakan ko kadan bai dace ba.(Ibrahim)

Ibrahim