logo

HAUSA

Fararen Hular Afghanistan Nawa Ne Sojojin Amurka Za Su Kashe?

2021-08-31 13:53:10 cri

A yammacin ranar 29 ga wata, sojojin Amurka da ke Afghanistan sun yi amfani da jiragen sama marasa matuka wajen kai hari wata unguwar dake Kabul. Harin ya kashe fararen hula 10, wanda mafi karancin shekarunsu bai wuce shekaru 2 ba kacal.

Da farko, kasar Amurka ta yi ikirarin cewa harin da ta kai ta sama ya kashe wani dan ta’adda wanda ake “zaton’ yana da “shirin” kai harin kunar bakin wake na mota a tashar jirgin saman Kabul, amma ba da jimawa ba ta sauya kalamanta.

Sojojin Amurka sun bayyana cewa, sun yi harbe harbe kan wata motar da “wai” tana dauke da ‘yan ta’adda da dama daga kungiya mai tsattsauran ra’ayi, daga baya hare-haren “wanda ake zaton” ya tayar da boma-boman da ke cikin motar, sannan kuma fashewar bam ta biyu mafi girma ta haifar da asarar rayukan fararen hula.

Fararen Hular Afghanistan Nawa Ne Sojojin Amurka Za Su Kashe?_fororder_微信图片_20210831112523

Aikin kaddamar da hari saboda “shakka”, “wai” ya kasance abin mamaki ne, amma shin da gaske ne fashewar ta biyu ta haddasa asarar rayuka kamar yadda sojojin Amurka suka fada?

Lokacin da dan jaridarmu na babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin da ke Kabul ya isa inda abin ya faru, ya ga motar da aka harba tana cikin harabar gidan, kuma harbin ya shafi wata motar da ke kusa da ita. Matasa da dama suna tsaftace tarkacen motar, kuma abubuwan yau da kullum da yawa a cikin motar sun zama wadanda ba a iya tantance su gaba daya.

Wadanda lamarin ya auku kan idonsu sun tabbatar cewa, babu wani abu mai fashewa a cikin motar, kuma hakika babu alamun fashewa ta biyu a yankin da ke kewaye, saboda tsoffin gidajen ba sa iya jure tasirin babban fashewar. Iyalan wadanda abin ya rutsa da su sun nanata a cikin hirar da suka yi da yan jaridarmu cewa, dangoginsu 10 sun mutu a wannan tashin bam din. Wasu daga cikinsu suna shirye-shiryen bikin aurensu, wanda mafi karancin shekarunsu bai wuce shekaru 2 ba kacal.

Fararen Hular Afghanistan Nawa Ne Sojojin Amurka Za Su Kashe?_fororder_微信图片_20210831112528

A cewar iyalan wadanda abin ya rutsa da su, mai motar ya kasance wanda ke aiki a wata hukumar kasar waje kafin rasuwarsa, kuma an ba shi biza kafin harin, ya yi ta jiran hukumar ta shirya fitar da shi daga kasar, amma bayan kwanaki sama da 10 an tabbatar da matsayinsa na wai “dan ta’adda ne”. Fushin iyalan bai tsaya a nan kawai ba. Wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya sun zo nan kuma suna ta ci gaba da tambayarsu: “Ina ‘yan ta’addar kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta ‘IS'? Ko kun boye su?”

Motar dake farfajiyar wurin babu alamar fashewar ta biyu, yaron yana kwance cikin jini ... Gaskiyar hakikanin halin ya tabbatar da cewa, wannan bam ne mai kuskure tare da cikakkiyar shaida!

A cikin shekaru 20 da suka gabata, sojojin Amurka sun dade da yin kisan gilla da tada bama-bamai a kurkure a Afghanistan. Bayan fashewar bom da aka samu a filin jiragen saman Kabul a ranar 26 ga wata, sojojin Amurka sun yi luguden wuta kan mutanen ba tare da izini ba. A ranar 29 ga wata, sun kara tada bom kan gidajen fararen hula. To, fararen hular Afghanistan nawa ne sojojin Amurka za su kashe kafin su janye jiki dukkan fannoni daga kasar? (Mai fassara: Bilkisu)