logo

HAUSA

Geng Shuang: Ya dace a yi la’akari bayan janye sojoji daga Afghanistan

2021-08-31 10:57:40 CRI

Jiya Litinin ranar 30 ga wata, kwamitin sulhun MDD ya zartas da daftarin kudurin dake shafar batun kasar Afghanistan bisa kuri’un amincewa 13 ba tare da ko da kuri’ar nuna adawa ba, da kuma kuri’un kauracewa biyu da aka kada, inda kasashen Sin da Rasha ba su jefa kuri’a ba, daga baya mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang, ya yi nuni da cewa, yanayin da Afghanistan ke ciki yanzu yana da dangantaka da janyen sojojin kasashen waje daga kasar, yana fatan kasashen da abin ya shafa su yi la’akari kan batun, kuma su gyara kuskure a kan lokaci, a maimakon kammala aiki kawai.

Jami’in ya kara da cewa, ya dace kasashen da abin ya shafa su koyi dasari, kuma su martaba ikon mulkin kasar Afghanistan da ‘yancin kanta da kuma cikakkun yankunan kasar, haka kuma su nuna biyayya ga hakkin al’ummun kasar na yanke shawara kan makomar kasarsu, a sa’i daya kuma, su gyara kuskuren da suka yi, har su daina daukar matakan nuna karfin tuwo ta hanyar matsin lamba ko saka takunkumi.(Jamila)