logo

HAUSA

Sin ta janye jiki daga jefa kuri’u kan kudurin kwamitin sulhun MDD kan batun Afghanistan

2021-08-31 20:00:58 CRI

Sin ta janye jiki daga jefa kuri’u kan kudurin kwamitin sulhun MDD kan batun Afghanistan_fororder_wang

A kwanakin baya, Sin ta janye jiki daga jefa kuri’u kan kudurin kwamitin sulhun MDD game da batun Afghanistan.

Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau cewa, Sin ta nuna shakku ga wajibci da hanzarin amincewa da kudurin da ma daidaito kan abubuwan da ya kunsa. Haka kuma kasar Sin ta ki amincewa da yadda wadanda suka gabatar da kudirin tilasta zartar da shi, yayin da bangarori daban daban ke da bambancin ra’ayi

Rahotanni na cewa, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kudurin da Amurka da Birtaniya da Faransa suka gabatar, inda aka bukaci kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan da ta cika alkawari, da bar ‘yan kasar da na kasashen waje su bar Afghanistan, kuma Sin da Rasha sun janye jiki daga jefa kuri’u kan kudurin. (Zainab)