logo

HAUSA

Xi Jinping ya zanta da takwaransa na Malawi ta wayar tarho

2021-08-27 21:44:12 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Malawi Lazarous Chakwera ta wayar tarho a yau Jumma’a.

A yayin zantawar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tun lokacin da Sin da Malawi suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, dangantaka tsakanin kasashen biyu ta rika ci gaba cikin sauri ba tare da wata matsala ba. Kana bangarorin biyu sun hada hannu don yakar annobar COVID-19, hadin gwiwar na ci gaba da samun ingantuwa. Kasar Sin tana son karfafa hadin kai tare da Malawi a wannan fanni, kuma tana fatan alluran riga kafin annobar da kasar Sin ta ba ta zai taka rawar gani a yakin da Malawi ke yi da cutar.

Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin ta yaba da yadda Malawi ta martaba manufar Sin daya tak a duniya, tana kuma goyon bayan Malawi wajen zabar hanyar raya kasa da ta dace da yanayin da take ciki, kuma a shirye take ta ci gaba da baiwa Malawi taimako da goyon baya, don ciyar da tattalin arziki da zamantaker al’ummarta gaba.

A nasa jawabin, shugaba Chakwera ya sake taya JKS murnar cika shekaru 100 da kafuwa da kuma nasarori na tarihi da kasar ta cimma a fannin warware matsalar talauci. Yana kuma godewa kasar Sin kan taimakon da take baiwa Malawi ta fuskar yakar annobar COVID-19. A cewarsa, jarin da kasar Sin take zubawa a kasar da hadin gwiwar da ta kulla, sun taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar kasar ta Malawi. Haka zalika ya ce, kasarsa tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, tana kuma adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe ta hanyar amfani da batutuwan kare hakkin dan Adam, da siyasantar da batun asalin cutar COVID-19. (Bilkisu)