logo

HAUSA

Kungurmin dajin da Xi Jinping ke mai da hankali a kai

2021-08-25 14:32:18 CMG

Kungurmin dajin da Xi Jinping ke mai da hankali a kai_fororder_daji-1   Kungurmin dajin da Xi Jinping ke mai da hankali a kai_fororder_daji-3

Kungurmin dajin da Xi Jinping ke mai da hankali a kai_fororder_daji-2   Kungurmin dajin da Xi Jinping ke mai da hankali a kai_fororder_daji-4

Ranar 25 ga watan Agusta, rana ce ta musamman da gwamnatin kasar Sin ta kebe don yayata ra’ayin rage fitar da iska mai dumama yanayi. Kafin wannan rana ta bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kungurmin dajin Sai-Han-Ba dake arewacin lardin Hebei na kasar Sin.

Dalilin da ya sa shugaban ya yi rangadi a dajin, shi ne domin yabawa dimbin ma’aikatan da suka kwashe shekaru fiye da 50 suna kokarin dasa itatuwa a Sai-Han-Ba, inda aka samu nasarar sauya wata hamada zuwa kungurmin daji.

A cewar shugaba Xi, dole ne a yi kokarin gado da yayata ruhin Sai-Han-Ba, don raya tattalin arziki da al’adu masu alaka da kare muhallin halittu. (Bello Wang)

Bello