logo

HAUSA

Xi Jinping ya kai ziyarar aiki gandun dajin Saihanba

2021-08-24 11:05:00 CRI

Xi Jinping ya kai ziyarar aiki gandun dajin Saihanba_fororder_1

Babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyarar aiki gandun dajin Saihanba dake lardin Hebei na kasar Sin, inda ya duba yanayin gandun dajin, da kuma sauraron rahoto game da yadda ake inganta aikin kare muhalli da kiyaye gandun dajin, a sa’i daya kuma, ya gana da masu kare gandun dajin.

Yankin Saihanba ya taba zama wuri mai ni’ima, inda yake da albarkatun tsirrai da koguna, amma, ya sauya zuwa Hamada a farkon karni na 20. Shi ya sa, a shekarar 1962, kasar Sin ta tsai da kudurin kafa gandun daji mai fadi a wannan yanki, kuma, bayan an yi shekaru 59 ana kokari a wannan yanki, yanzu, an cimma nasarar kafa gandun dajin da fadinsa ya kai kimanin muraba’in mita miliyan 767, wanda ya zama gandun daji mafi fadi da mutane suka kafa a duniya. (Maryam)