logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Tsarin Demokuradiya Na Kasar Sin Babbar Nasara Ce Wajen Tafiyar Da Harkokin Kasa Da Kasa

2021-08-10 19:50:20 CRI

Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya Charles Onunaiju, ya bayyana cewa, tsarin demokuradiya na kasar Sin, yana daya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma, a ayyukan tafiyar da harkokin kasa da kasa.

Charles Onunaiju ya bayyana haka ne, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Yana mai cewa, ci gaba da kasar Sin ta samu da karfinta na tunkarar duk wasu matsaloli, suna da nasaba da imanin da jama’arta ke da shi kan tsarin shugabancinta, abin da ke nuna cewa, kasar Sin ta samu tsarin demokuradiyar da ya dace da yanayin kasa da kuma al’ummarta.

Onunaiju ya kuma yi imanin cewa, yadda ‘yan kasar suka gamsu, da ma imani da gwamnatinsu, suke auna ingancin tsarin demokuradiyar kasar, kuma irin wannan tsari a cewarsa, ya yi tasiri wajen nuna karfin wayin kan Sinawa, bisa la’akari da kokarin kasar na yakar talauci da yaki da annobar COVID-19.

Ya kara da cewa, abu mafi muhimmanci ga tsarin demokuradiya na kasar Sin, shi ne yadda ake mayar da jama’a a gaban komai. Yana mai nuni da cewa, taron wakilan jama’ar kasar Sin da taron majalisar ba da shawawa kan harkokin siyasar kasar Sin, taruka biyu ne, da suka kunshi bangarori daban-daban na zamantakewa, kana tsarin demokuradiya ne da ake tattauna batutuwa da kusan ya kunshi kowa. Wakilan dake halartar tarukan biyu, suna da tsare-tsare da dandaloli na tattaunawa da mutanen da suke wakilta, inda suke zama kamar wata gada, dake hada ra’ayoyin jama’ a da manufofi na gwamnatin tsakiya. A don haka, kowa yana shiga a dama da shi wajen yanke shawara da ta shafi kasa. Masanin ya kuma yi imanin cewa, Afirka, wadda ke mu’amala da kasar Sin, tana iya koyon wadannan tsare-tsare daga gare ta.(Ibrahim)

Ibrahim