logo

HAUSA

Rahoto: Kamfanonin kasar Sin na taimakawa tattalin arzikin Afirka samun ci gaba daga dukkan fannoni

2021-08-27 10:51:31 CMG

Rahoto: Kamfanonin kasar Sin na taimakawa tattalin arzikin Afirka samun ci gaba daga dukkan fannoni_fororder_2

A jiya Alhamis, an gabatar da wani rahoto mai taken “Yadda kamfanonin kasar Sin suke zuba jari a nahiyar Afirka” a birnin Beijing na kasar Sin. Cikin rahoton, an ce, yayin da kamfanonin kasar Sin suke zuba jari a kasashen Afirka, suna samar da gudunmowa ga ayyukan raya masana’antu, da kyautata zaman rayuwar jama’a, ta yadda suke taimakawa samun ci gaban tattalin arziki daga dukkan fannoni a nahiyar Afirka.

Justin Yifu Lin, wani shahararren shehun malami mai nazarin tattalin arziki na jami’ar Peking na kasar Sin, ya bayyana yayin da yake halartar bikin gabatar da rahoton cewa, yadda kamfanonin kasar Sin suke zuba jari a nahiyar Afirka na haifar da moriya ga dukkan Sin da Afirka, saboda zuba jarin da ake yi, ya sa ana samun ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da samar da kudi da fasahohi ga kasashen Afirka, ta yadda za su samu damar sarrafa albarkatunsu.

A nashi bangare, jakadan kasar Habasha dake kasar Sin Teshome Toga Chanaka ya ce, kamfanonin kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a fannin zamanintar da kayayyakin more rayuwa a kasashen Afirka, gami da aikin farfado da tattalin arzikin nahiyar.

Duk a wajen bikin kadammar da rahoton, Vera Songwe, sakatariyar zartaswar ta hukumar kula da tattalin arzikin Afirka na MDD, ta ce, kamfanonin Sin na ci gaba da kokarin zuba jari a kasashen nahiyar, duk da yanayin bazuwar cutar COVID-19 da ake fuskanta a duniya, lamarin da ya ba kasashen Afirka damar samun karin guraben ayyukan yi. (Bello Wang)

Bello