logo

HAUSA

Gwamnatin Kamaru ta tura sojoji domin kwantar da tarzoma a yankin arewa mai nisa na kasar

2021-08-13 11:25:46 CMG

Gwamnatin Kamaru ta tura sojoji domin kwantar da tarzoma a yankin arewa mai nisa na kasar_fororder_1

Gwamnan jihar arewa mai nisa ta kasar Kamaru Midjiyawa Bakari, ya ce gwamnatin tarayya ta tura sojoji zuwa yankin domin dawowa doka da oda, sakamakon wani fadan kabilanci da ya sabbaba kisan mutane 12, tare da raunata wasu a kalla 48, baya ga gidaje sama da 100 da aka kone kurmus.

Gwamna Bakari, wanda ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na Xinhua hakan a jiya Alhamis, ya ce wani rashin jituwa ne ya auku a ranar Talata a garin Kousseri, tsakanin masuntan yankin Mousgoum, da makiyayan yankin Arabchoas, game da wurin da suke samun ruwa, lamarin da ya rikide zuwa mummunan tashin hankali.

A cewar gwamnan, wakilan gwamnati da na jami’an tsaro, tare da shugabannin al’ummar yankin sun amince da kafa wani kwamitin bincike, wanda zai ziyarci wuraren da tashin hankalin ya rutsa da su, da nufin dakile yanayi na zaman dar dar, tare da gudanar da sulhu.

Da ma dai yankin mai makwaftaka da Logone da Chari, ya sha fuskantar dauki ba dadi da zubar da jini tsakanin kabilu mazaunan sa cikin shekaru 5 da suka gabata, to sai dai kuma tashin hankalin da ya auku a ranar Talata shi ne mafi kazanta da aka taba gani a yankin, kamar dai yadda rahoton jami’an tsaro ya tabbatar.  (Saminu)

Saminu