logo

HAUSA

An yi kira da a kare Zakuna a Afrika yayin da suke fuskantar karin barazana

2021-08-11 11:15:52 CMG

An yi kira da a kare Zakuna a Afrika yayin da suke fuskantar karin barazana_fororder_4

Shugaban gangamin kare namun daji na kungiyar kare dabbobi ta duniya reshen Afrika, Edith Kabesiime, ya ce zaki a nahiyar Afrika na fuskantar barazana daban-daban, don haka akwai bukatar karfafa kare shi.

A cewarsa, yanayi da ayyukan bil adama, sun kara ta’azzarar barazanar da babbar dabar ke fuskanta a shekarun baya-bayan nan.

Ya ce Zaki na da daraja a galibin al’adun Afrika, amma rayuwarsa na fuskantar barazana saboda farauta ba bisa ka’ida ba, da lalacewar muhalli da raguwar namun da yake farauta da hare-haren makiyaya.

Alkaluma daga kungiyar kare dabbobi ta duniya sun nuna cewa, yawan zakuna a Afrika ya tsaya ne kan 20,000, adadin da ya ragu daga miliyan 2 cikin shekaru 100 da suka gabata, yayin da raguwar ka iya haifar da rashin daidato tsakanin yanayin muhalli da halittu.

Edith Kabesiime, ya ce ya kamata ranar kare zaki ta duniya ta bana, ta zaburar da gwamnatoci da masu ruwa da tsaki da al’ummomi, kan bukatar farfado da matakan tunkarar barazanar da dabbar mai daraja ke fuskanta.

Hadaddiyar kungiyar kare halittu ta duniya, ta ayyana zakin Afrika a matsayin mai rauni dake fuskantar farautar da ta sabawa doka da kutse a muhallinsa da kuma matsalolin yanayi.

A cewar Edith Kabesiime, tuni zakuna a yammacin Afrika ke cikin hadari mai tsanani, yayin da farautarsu ke karuwa a fadin yankunan gabashi da kudancin nahiyar. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza