logo

HAUSA

Sin: Gaskiya za ta bayyana game da karairayin da wasu ke yadawa kan Xinjiang

2021-06-29 19:42:29 CRI

Sin: Gaskiya za ta bayyana game da karairayin da wasu ke yadawa kan Xinjiang_fororder_新疆好地方

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, Karya fure take ba ta ‘ya’ya. Haka kuma ko ba dade ko ba jima, gaskiya za ta fito fili, dangane da karairayin da wasu mutane ke yadawa game da jihar Xinjiang ta kasar Sin, duba da irin shaidu da bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’umma da ma yadda dukkan kananan kabilun yankin ke zaune cikin farin ciki.

Rahotanni na cewa, cibiyar nazarin harkokin siyasa, zamantakewar al’ummar kasa da tattalin arziki ta kasar Italiya, da cibiyar harkokin diflomasiyar kasa da kasa ta Italiya da cibiyar nazarin harkokin Turai da Asiya da yankin Meditareniya ta Italiya, sun fitar da wani rahoton bincike na hadin gwiwa mai taken “ Xinjiang: fahimtar yanayi mai sarkakkiya da gina zaman lafiya”. Mutumin da ya rubuta wannan rahoto, ya bayyana cewa, bai ga wata shaida dake nuna cewa, wai ana tilasta “aikin kwadago da kisan kiyashi” a Xinjiang ba, haka kuma babu wata shaida game da zargin wasu matsaloli da kasashen yamma ke yi a yankin na Xinjiang.(Ibrahim)

Ibrahim