logo

HAUSA

Yadda kasashen yamma suke fakewa da batun hakkin dan Adam don ta da rikici a duniya

2021-07-05 15:41:33 CMG

Yadda kasashen yamma suke fakewa da batun hakkin dan Adam don ta da rikici a duniya_fororder_20210705-Biafra-Bello

A kwanakin nan, an tusa keyar Nnamdi Kanu, madugun kungiyar Biafra, zuwa kasar Najeriya. Wannan wani labari ne mai kyau ga kasar, sai dai wasu kafofin watsa labaru da hukumomi na kasashen yammacin duniya sun nuna wani ra’ayi na daban.

Kamar yadda kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka saba yi ne, inda maimakon bayyana ra’ayinsu kai tsaye, sun tsamo maganganu da wasu mutane suka fada, don bayyana ra’ayoyi a madadinsu. A wannan karo, kamfanin dillancin labaru na kasar Amurka Bloomburg ya watsa wani bayani mai taken “An kama Nnamdi Kanu ta wata haramtaciyar hanya”, inda ya tsamo maganar mutanen wani kamfanin kasar Amurka, wanda Nnamdi Kanu ke hulda da su, don hurewa ‘yan majalisun kasar Amurka kunne, ta yadda za su ba kungiyarsa taimako. Kana wadannan mutane sun ce hanyar da gwamnatin kasar Najeriya ta bi wajen kama Kanu ta karya doka. Ta wannan bayani, kamfanin Bloomburg na son bayyana ra’ayinsa, wato: Ko da yake Kanu ya dade yana neman balle yankin kudu maso gabashin kasar Najeriya, kana ya kafa kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta ESN; ko da yake, gwamantin Najeriya ta taba kama shi bisa zarginsa da laifuka da yawa, ciki har da cin amanar kasa, kana daga bisani ya samu damar tserewa zuwa ketare yayin da aka ba da shi beli, duk da haka yadda gwamnatin Najeriya ta kama shi a wannan karo ya kasance “karya doka”, inda aka keta hakkinsa na dan Adam. A nan ina so in yi tambaya: Ta yaya ne za a kare hakkin dan Adam na sojoji da ‘yan sanda da dakarun kungiyar ESN suka kashe? Ko ‘yan sanda da sojoji ba su cancanci a kare hakkinsu ba?

A lokaci guda, wata kungiyar kasar Amurka mai suna “Coucil of Foreign Relationship”, wadda ta bayyana kanta a matsayin kungiya mai zaman kanta, ta wallafa wani bayani a shafin yanar gizo nata, mai taken “Bai kamata ba a ta da yakin basasa don kiyaye ‘yan kabilar Igbo”, inda aka ce wata kungiyar kasar Najeriya mai suna “Northern Elders Forum” ta yi kira da a ba da mutanen kabilar Igbo damar balle yankin kudu masu gabashin Najeriya daga kasar, don magance sake ta da wani yakin basasa. Ta hanyar tsamo wannan magana, kungiyar CFR ta kasar Amurka na son bayyana ra’ayinta cewar: A maimakon a yi kokarin dakile mutanen dake yunkurin janyowa kasar Najeriya baraka, da haddasa zub da jini a kasar, ya kamata a ba su damar ballewa daga kasar. Gaskiya wannan kirayi ya ba ni mamaki sosai, domin ban taba ganin wata kasa da za ta iya hakuri kan yadda aka lahanta mulkin kanta da cikakken yankinta kamar haka ba. Idan an ba yankin kudu maso gabashin Najeriya damar ballewa daga kasar, to, yakin basasa da aka yi a kasar tsakanin shekarar 1967 da ta 1970, wanda ya haddasa rasa rayukan mutane fiye da miliyan 2, ya zama babu ma’ana ko kadan.

Sai dai wadannan bayanan da aka wallafa sun nuna wani buri na musamman da kasashen yammacin duniya ke da shi a fannin batun hakkin dan Adam, wato suna fakewa da “kare hakkin dan Adam”, don ta da rikice-rikice da matsaloli a sauran kasashe, maimakon ba su taimako. A wannan karo muna iya ganin cewa, kasashen yamma suna tsayawa tare da masu cin amanar kasar Najeriya, inda suke zargin gwamnatin kasar da karya doka, da nuna goyon baya ga yunkurin janyo wa kasar Najeriya baraka. Wato suna neman lahanta moriyar jama’ar kasar Najeriya.

A hakika, ba a Najeriya kadai su kasashen yamma suke yin haka ba.

A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2009, an samu abkuwar wani mummunan harin ta’addanci a birnin Urumqi, hedkwatar jihar Xinjiang ta kasar Sin, inda a karkashin jagorancin kungiyar “taron wakilan ‘yan kabilar Uygur na duniya” dake neman balle yankin Xinjiang daga kasar Sin, wasu ‘yan daba fiye da dubu 1 sun kaddamar da hare-hare a wurare daban daban na birnin, lamarin da ya haddasa hasarar rayukan mutane 197, da jikkatar wasu 1700. Daga bisani, wato bayan shekarar 2009, kusan a kowace shekara, masu neman ballewar jihar Xinjiang su kan kaddamar da hare-haren ta’addanci fiye da 100 a jihar. Bisa kwararan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka na dakile yunkurin balle Xinjiang da ayyukan ta’adanci, an samu kwantar da kurar da ta tashi a jihar ne sannu a hankali. Cikin shekaru fiye da 4 da suka wuce, ba a sake samun abkuwar wani harin ta’addanci a jihar Xinjiang ba. Amma su mutanen kasashen yamma ba su lura da yadda aka dawo da kwanciyar hankali da zaman walwala a jihar Xinjiang ba, maimakon haka sun ce wai an “keta hakkin dan Adam” na wasu mutanen da suke neman balle Xinjiang daga kasar Sin. Suna ta kokarin yada jita-jita game da jihar Xinjiang, cewa wai gwamnatin kasar Sin tana “tursasa ‘yan Uygur da Musulmai”. Duk wani abun da gwamnatin kasar Sin ta yi ba zai zama daidai ba ne a idanunsu, illa kawai ta nade hannu, ta ba masu neman balle Xinjiang damar kai hare-hare, da balle jihar daga kasar Sin don kafa wata kasa mai taken “East Turkistan”. A zahiri ne, kasashen yamma suna fakewa da batun hakkin dan Adam, suna neman lahanta moriyar jama’ar kasar Sin.

Kar a yi tsammanin cewa kasashen yamma na bayyana ra’ayinsu ne kawai, a hakika suna kokarin samar da taimako ga kungiyoyin ‘yan aware na sauran kasashe. Misali, idan ba a manta ba, Nnamdi Kanu ya kasance dan kasar Birtaniya ne yanzu. Kana gidan radiyon Biafra da yake amfani da shi wajen watsa tunanin ballewar kasar, a birnin London yake. Sa’an nan bayan da aka kama shi a wannan karo, nan take gidan jakadancin kasar Birtaniya dake Najeriya ya ce zai samar masa da hidima da kariya a fannin kulawar da ake yiwa ‘yan kasa. Kana a nata bangare, kungiyar ‘yan aware ta “Taron wakilan ‘yan Uygur na duniya” dake neman balle Xinjiang daga kasar Sin na samun kudi daga asusun dimokuradiya na kasar Amurka NED a kai a kai.

Ta da rikici a sauran kasashe, da janyo musu baraka, wannan shi ne babban makasudin kasashen yammacin duniya, yayin da suke fakewa da batun hakkin dan Adam. Kowa ya ga yadda suke kokarin “kare hakkin dan Adam” a kasashen Iraki, da Afghanistan, da Libya, da dai sauransu. Saboda haka, idan kasashen yamma suka sake tada takaddama game da hakkin dan Adam, bari mu yi nazari kan ainihin burinsu, maimakon amincewa da jita-jitar da suke kokarin yadawa. (Bello Wang)

Bello