logo

HAUSA

Ci Gaban Xinjiang Ya Sake Musunta Karyar Kasashen Yammacin Duniya

2021-07-16 13:50:23 CRI

Ci Gaban Xinjiang Ya Sake Musunta Karyar Kasashen Yammacin Duniya_fororder_xj

Ranar 14 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani, wadda ta kunshi bayanai game da ci gaban da aka samu dangane da kare hakkokin kabilun jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin. *****

Takardar mai taken “Martabawa da Kare Hakkokin Dukkan Kabilun Jihar Xinjiang” ta bayyana yadda ake kiyaye hakkokin ‘yan kabilu daban daban na Xinjiang bisa doka, a matsayin ‘yan kasa a fannonin siyasa, tattalin arziki, al’adu, addinai daga dukkan fannoni. Takardar ta ce, sakamakon yadda JKS da gwamnatin kasar suke mayar da hankali kan kare hakkokin jama’a a gaban komai, ya sa Xinjiang ta samu gagarumin ci gaba a fannin kare hakkin dan Adam. Lamarin da ya sake musunta karyar masu adawa da kasar Sin daga kasashen yammacin duniya.

Yin adalci a tsakanin mabambantan kabilu, yana daya daga cikin muhimman ka’idojin jamhuriyar jama’ar kasar Sin tun bayan kafuwarta. Takardar ta yi karin bayani da cewa, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin har zuwa yanzu, kasar tana tsayawa kan yiwa kabilu adalci, da hada kan kabilu, da kara azama kan ci gaban kabilu, yayin da take tinkarar batutuwan kabilu da huldar da ke tsakanin kabilunta.

A shekarar 1955 ne aka kafa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, inda ‘yan kabilu daban daban suke shiga harkokin kasa, da na jihar cikin adalci, tare da aiwatar da dama da salon mulkin dimokaradiyya ya tanada, lamarin da ya aza harsashi mai kyau a fannin bunkasar hakkin dan Adam a Xinjiang.

‘Yan aware na kungiyar ta’addanci ta East Turkestan Islamic Movement a gida da wajen kasar Sin, sun taba daukar tsawon lokaci suna hada hannu wajen kai hare-haren ta’addanci dubai a Xinjiang, wadanda suka kawo mummunar barazana ga rayukan ‘yan kabilun Xinjiang da ‘yancinsu. Saboda haka gwamnatin Sin ta dauki matakan yaki da ta’addanci da dama, wadanda suka samu sakamako mai kyau. Tun daga karshen shekarar 2016 har zuwa yanzu, a shekaru fiye da 4 ne a jere babu wani harin ta’addanci a Xinjiang. Jihar ta Xinjiang ta kama hanyar samun saurin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa da ma zaman rayuwar jama’a.

Idan ba a samu bunkasuwa ba, to, ba za a iya kare hakkokin dan Adam ba. Takardar ta yi bayani da cewa, sakamakon jerin matakan yaki da talauci da ake dauka, ya sa ya zuwa karshen shekarar 2020, an fitar da dukkan mutane miliyan 2 dubu 730 a yankunan karkara daga kangin talauci da suka yi fama da shi a Xinjiang. A karon farko an kawar da talauci a jihar ta Xinjiang a tarihinta. Kuma a jihar Xinjiang, dukkan kabilu na da damar samun ci gaba cikin adalci. Manufar samun ci gaba ita ce samun wadata tare.

Har ila yau ana kiyaye da raya al’adun kabilu da ‘yancin bin addini a Xinjiang. Yanzu ana amfani da yaruka da kalmomi fiye da 10, na kabilun Xinjiang a zaman yau da kullum. Ko da yake wasu mutanen kasashen yammacin duniya sun yi ta maimaita karyar wai ana tilasta rushe masallatai a Xinjiang, amma a gaskiya ita ce, an tanadi kayayyaki isassu a masallatan Xinjiang, ciki har da likitoci, allon wutar lantarki, kwamfuta da dai sauransu, wadanda suka bai wa musulmai sauki sosai.

Ban da haka kuma, masu adawa da kasar Sin na kasashen yammacin duniya sun yi ta baza wata karya ta daban, wato wai an yi kisan kiyashi a Xinjiang. Hakika dai a shekaru 40 da suka wuce, yawan ‘yan kabilar Uygur ya karu zuwa miliyan 12 da dubu 800, daga miliyan 5 da dubu 500 a Xinjiang, yayin da matsakaicin tsawon rayukan ‘yan kabilar ya karu zuwa 72 daga 30.

A halin yanzu, jihar ta Xinjiang tana cikin lokaci mafi samun ci gaba a tarihinta. Bisa abubuwan da suke faruwa a Xinjiang, kasashen duniya za su kara fahimtar yadda kasar Sin take yin adalci a tsakanin mabambantan kabilu, tare da rika kyautata kiyaye hakkin dan Adam.

Wasu wadanda suka kira kansu masu rajin kare hakkokin bil Adama a kasashen yammacin duniya ba za su samu nasarar hana ci gaban kasar Sin ta hanyar tada kura a Xinjiang ba. Ya dace su yi tunanin yadda za su biya bashi a fannonin nuna bambancin launin fata, da yin mulkin mallaka. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan