Kasar Sin ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a Afghanistan
2021-08-27 20:36:48 CRI
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labaran da aka saba shiryawa Jumma’ar nan cewa, kasarsa ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a kasar Afghanistan, ta kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa tare da jajentawa wadanda suka jikkata da ma iyalansu.
A jiya ne dai, aka samu fashewar wasu abubuwa guda biyu a kusa da filin jirgin saman Kabul, babban birnin Afghanistan, lamarin da ya haddasa asarar rayukan mutane masu yawa. Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin lamarin.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan wannan batu, Zhao Ljian, ya ce, kasar Sin tana adawa tare da yin Allah wadai da duk wani nau’i na ayyukan ta’addanci, tana kuma fatan yin aiki da kasashen duniya wajen yaki da barazanar ta’adanci tare da hana Afghanistan sake zama tungar ‘yan ta’adda.