logo

HAUSA

Fiye da kashi 80% na mutane masu amfani da Internet na ganin cewa gwamnatin kasar Amurka ta sha kunya a Afghanistan

2021-08-27 15:22:16 CMG

Fiye da kashi 80% na mutane masu amfani da Internet na ganin cewa gwamnatin kasar Amurka ta sha kunya a Afghanistan_fororder_210827-CGTN-Iraki-Bello4

Kungiyar kwararru karkashin kamfanin CGTN ta kaddamar da binciken ra’ayin jama’a a shafin yanar gizo, a ranar 20 ga watan da muke ciki, inda ta yi wa mutanen da suka shiga binciken tambayar cewa “Shin kana ganin yakin da kasar Amurka ta kaddamar a Afghanistan ya ci tura? ”, kashi 84.6 daga cikin mutanen sun ba da amsa cewa, a ganinsu gwamnatin kasar Amurka ta sha kunya.

Har wasu ma sun ce “Dukkan kasar Amurka da sauran kasashen yammacin duniya sun sha kunya”. Wani mai amfani da yaren Ingilishi ya ce, “Bisa dalili na son kai, kasar Amurka ta lalata kasashen Iraki, da Libya, da Sham, da kuma Afghanistan. Shaidanun manufofin kasar Amurka ne suka sa hakan ya faru.”

Sauran mutane da yawa sun nuna shakku kan dalilin da ya sa kasar Amurka ta kaddamar da yaki a Afghanistan. A ganinsu an yi yakin ne ba domin yakar ta’addanci, ko kuma taimakawa jama’ar Afghanstan ba, kawai Amurka ta nemi yin mulki mallaka a Afghanistan ne don biyan bukatunta. Alkaluman da MDD ta gabatar sun nuna cewa, daga shekarar 2009 zuwa ta 2019, fararen hula da suka rasa rayuka ko suka ji rauni a kasar Afghanistan sun zarce dubu 100.(Bello Wang)

Bello