logo

HAUSA

Mai sarrafa jirgin sama maras matuki na Amurka ya gabatar da bidiyon kashe fararen hular Afghanistan

2021-08-26 11:26:34 CRI

Mai sarrafa jirgin sama maras matuki na Amurka ya gabatar da bidiyon kashe fararen hular Afghanistan_fororder_hoto2

Kwanan baya, wani mai aikin sarrafa jirgin sama maras matuki na kasar Amurka Jack Murphy ya gabatar da bidiyo kan yadda sojojin Amurka suka gudanar da matakan soja a kasar Afghanistan. Cikin wadannan shirye-shiryen bidiyon da ya gabatar, an gano cewa, a shekarar 2019, sau da dama, sojojin Amurka suka kai hare-haren sama a sassan kasar Afghanistan, wadanda suka haddasa rasuwar fararen hula da yawa, ciki har da mata da yara.

Jack Murphy ya ce, adadin da kasar Amurka ta gabatar game da rasuwar mutanen kasar Afghanistan sakamakon hare-haren da ta kaddamar, kadan ne daga cikin ainihin adadin mutanen da suka mutu. Ya kuma kara da cewa, “an kai hare-hare domin kashe mutane”.

Wani mai aikin sarrafa jirgin maras matuki na kasar Amurka daban, wanda bai fadi sunansa ba, ya ce, ya ji raunin kwakwalwa mai tsanani sakamakon wani kisan kuskuren da ya yi a shekarar 2019. Ya ce, a lokacin, an ba da umurnin kashe wani dan kasar Afghanistan mai amfani da rediyo, amma, wannan harin da suka kai masa, ya haddasa rasuwar sauran mutane guda biyu da kuma yaro daya. Kana, ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta sanar cewa, harin ya haddasa rasuwar mutum daya ne kawai.

A shekarar 2020, ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta bayyana cewa, hare-hare ta sama da kasar Amurka suka kai kasar Afghanistan a shekarar 2015 bai kai sau dubu 1 ba. Amma, a shekarar 2019, adadin ya ninka sau 6, wanda ya kai sau 7423. (Maryam)