Birtaniya za ta ci gaba da kwashe mutanenta a Afghanistan duk da fashewar bam a filin jirgin saman Kabul
2021-08-27 11:05:55 CRI
Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya sanar a jiya Alhamis cewa, kasar Birtaniya za ta ci gaba da aikin kwashe mutanenta daga filin jirgin saman Kabul, duk da fashewar tagwayen bama boman da ya faru.
A cewar firaministan, a bayyane take, abin da wannan harin yake nunawa shi ne, akwai bukatar a gaggauta gudanar da aikin kwashe mutane daga kasar a cikin ‘yan awoyin da suka rage musu, kuma wannan shi ne abin da ya dace a yi, ya kara da cewa, Birtaniya za ta ci gaba da gudanar da aikin har zuwa wa’adi na karshe.
Kasa da mako guda ya ragewa dakarun da Amurka ke jagoranta su fice daga kasar Afghanistan. A lokacin taron kolin kasashen G7 ta kafar bidiyo a ranar Talata, Johnson da sauran shugabannin kawayen Amurka sun gaza shawo kan shugaban kasar Amurka Joe Biden, da ya amince da tsawaita wa’adin kwashe jami’an daga Afghanistan, wanda zai cika a ranar 31 ga watan Agusta.
Tun da farko mista Johnson ya fada cewa, sojojin Birtaniyan sun riga sun kwashe kusan mutane 15,000, wadanda galibinsu suka cancanci komawa kasar Birtaniya.(Ahmad)