logo

HAUSA

Dalilin Da Ya Sa JKS Ta Cimma Nasara Shi Ne “Jama’a”

2021-08-27 14:09:11 CRI

Dalilin Da Ya Sa JKS Ta Cimma Nasara Shi Ne “Jama’a”_fororder_0827-01

Jiya Alhamis, sashen fadakar da jama’a na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin ya gabatar da littafi mai taken “Nauyin da JKS ta dauka da kuma gudummawar da ta bayar”. Cikin wannan littafi, an yi bayani kan yadda JKS ta jagoranci jama’ar kasar Sin wajen neman bunkasuwa cikin hadin gwiwa cikin shekaru 100 da suka gabata, domin cimma burin farfadowar kasa baki daya. Wato JKS ta samo asali ne daga jama’a, sannan tana dogaro da jama’a, da kuma yin ayyuka domin jama’a.

Wannan littafi ya kunshi kalmomin Sinanci fiye da dubu 40, wanda ya yi bayani game da tarihin kokarin jam’iyyar kwaminis ta Sin na shekaru 100 bayan kafuwarta, tare da tunaninta na aiwatar da harkokin siyasa da ayyukanta da kuma burin da ta cimma. A cikin littafin, bayani game da dangantakar dake tsakanin JKS da jama’ar kasar Sin ya fi burgewa sosai. Ta wannan, kasa da kasa za su kara fahimta yadda JKS ta fito da burinta, da kuma dalilin da ya sa yawan magoya bayan gwamnatin Sin ya kai matsayin koli a duniya bisa binciken da manyan hukumomin jin ra’ayoyin jama’a na duniya suka yi a shekaru da dama a jere.

JKS tana bin ra’ayin Marxism, an kafa ta a yayin da jama’ar kasar Sin suka yi yaki da tsarin mulkin malaka’u da yakin da bai cancanta ba, don haka jama’a fararen hula su ne tushen JKS. An kiyaye aikin kawo moriya ga jama’a fararen hula, da kin amincewa da duk aikin da zai kawo illa ga jama’a fararen hula, wannan ka’ida ce da JKS take bi a yayin neman ’yancin kai, da gina kasa, da kuma kwaskwarima a kasar, ta hakan burin kokarin JKS ya dace da bukatun jama’a. A hakika dai, dukkan membobin JKS fararen hula ne, tun daga lokacin kafuwarta da take da membobi 50 da wani abu kawai zuwa yanzu da take da membobi fiye da miliyan 95, wadanda suke la’akari da ra’ayin sauran jama’a wajen bada jagoranci. Don hakan, JKS tana kan gaba a duniya, kana tana dogaro da jama’a fararen hula da warware matsaloli da cimma nasarori daya bayan daya.

Tun daga cimma nasarar yakin masu kai hare-hare, zuwa kafa sabuwar kasar Sin, da kuma sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima, da kuma a yanzu cimma burin zaman al’umma mai matsakaicin karfi a dukkan fannoni, jama’ar kasar Sin sun yi kirkire-kirkire bisa jagorancin JKS, kuma sun kirkiro tarihi.

Game da batun yaki da cutar COVID-19, kokarin da jama’ar kasar Sin suka yi ya burge duniya sosai. Babban sakataren MDD António Guterres ya bayyana cewa, jama’ar kasar Sin sun sadaukar da kansu don hana yaduwar cutar COVID-19, wannan babbar gudummawa ce da suka samarwa dukkan dan Adam.

Masanin kwalejin ilmin zamantakewar al’umma na kasar Birtaniya Martin Albrow ya yi tsammani cewa, dalilin da ya sa jama’ar kasar Sin suka cimma nasarori a karkashin jagorancin JKS shi ne, ta kiyaye hidimtawa jama’a. Idan aka waiwayi kokarin da JKS ta yi a shekaru 100 da suka gabata, za a gano cewa ta yi hakan ne don sa kaimi ga jama’ar kasar su zama masu daukar nauyin kasa da zamantakewar al’umma da kansu, da jin dadin zaman rayuwarsu da kuma samun wadata tare.

Sin ta cimma nasarori da dama, misali, yawan kudin shigar kowanne mutumin kasar ya zarce dala dubu 10, kana yawan mutanen da suka samu matsakaicin kudin shiga a Sin ya fi girma a duniya, kana kafa tsarin bada tabbaci ga zamantakewar al’umma mafi girma a duniya, kuma Sin ta zama daya daga cikin kasashe mafi tsaro a duniya, wadanda suka shaida cewa, jama’ar kasar suna jin dadi, kuma JKS ta yi kokari cikin shekaru 100 wajen kyautata rayuwarsu. A halin yanzu, jama’ar kasar Sin na iya samun adalci a duniya, kana suna son samar da karin gudummawa ga zaman lafiya da bunkasuwar duniya baki daya.

Dalilin da ya sa JKS da ta kasance jam’iyyar da membobinta suka fi yawa a duniya ta cimma nasara shi ne, ta sanya moriyar jama’a fararen hula a gaban komai, kana jama’a fararen hula su ne tushen kirkire-kirkiren da aka yi don samun kyakkyawar makoma. Ana iya ganin cewa, duk yunkurin raba JKS da jama’ar kasar Sin, ko kuma kitsa adawa a tsakaninsu, ko sa jama’ar Sin yin watsi da JKS ba zai cimma nasara ba. (Zainab)