logo

HAUSA

Ba Wanda Zai Amince Da Rahoton Da Amurka Za Ta Bayar Kan Asalin Kwayar Cutar COVID-19

2021-08-25 17:00:08 CRI

Ba Wanda Zai Amince Da Rahoton Da Amurka Za Ta Bayar Kan Asalin Kwayar Cutar COVID-19_fororder_下载

Daga Amina Xu

A watan Mayun bana, shugaban Amurka Joe Biden ya yi shelar baiwa sassan leken asiri umurnin gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19 don tabbatar da cewa, ko kwayar ta fito daga dakin gwajin kwayoyin halittu ko a’a, tare da mika masa wani rahoto cikin kwanaki 90. Kwanan baya, akwai kafofin yada labarai da suka ruwaito cewa, sassan leken asiri ba su samu ci gaba a aikin ba, duk da haka, Amurka ta kare aniyar gabatar da rahoto kan lokaci tare da bayyana cikin rahoton cewa, kwayar ta samo asali ne daga dakin gwajin kwayoyin halittu na Wuhan. A ganin wasu ‘yan siyasar Amurka, ba don gano gaskiyar lamarin ba ake gudanar da bincike, ingiza a yi bincike kan wannan batu shi ne abin da suke so, da nufin kawo barazana ga kasar Sin a fannin diplomasiyya da matsa lamba kan kasar. Don haka, idan sassan leken asiri na Amurka sun gabatar da rahoto irin wannan, lalle babu wani abun mamaki ko kadan, saboda idan an waiwayi tarihin sassan leken asiri na kasar na yada jita-jita da gabatar da sakwannin sirri na jabu, to wa zai amince da irin rahoton da hukumar za ta bayar?

“Mun yin karya, da damfara, da kuma sata, kuma su ne matakan samun bunkasuwar Amurka”, in ji Mike Pompeo, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka, wanda ya taba zama shugaban babbar hukumar leken asiri ta kasar(CIA), wanda kuma ya bayyana aikin hukumar kamar haka. Bari mu duba yadda wannan hukuma ta yi karya da yada jita-jita.

Sanin kowa ne Amurka ta tada yaki a kasashen Iraqi da Sham bisa sakwanni na jabu. Garin wanke tufafi ya zama shaidu nazarin makamai masu guba har ya zama hujjar tada yaki a kasar Iraqi, baya ga kuma wani bidiyon da kungiyar Syrian Civil Defence ta kirkira ya zama sakon sirri don tada yaki a kasar Sham. Kirkirar sakwannin jabu da yin karya da yada jita-jita sun zama makaman hukumar na tada yake-yake da tada zaune tsaye a duniya. Ba shakka, ingiza binciken gano asalin kwayar cutar a zagaye na biyu a kasar Sin, hujjar da Amurka take amfani da shi ne don dora laifi kan kasar Sin.

A wani bangare kuma, sassan leken asairi na Amurka na da kwarewa sosai wajen yada labarai na jabu da yin tasiri kan kafofin yada labarai. Shirin da aka san shi da sunan “Operation Mockingbird” da Amurka ta tsara ta zama shaida, shiri ne dake kulla hulda da wasu ‘yan jarida ko hukumomi don neman yin tasiri kan yadda ake yada labarai. A shekarar 2014, Udo Ulfkotte, wani dan jarida na jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta kasar Jamus ya wallafa wani littafi mai taken “’Yan jarida da aka kulla hulda da su”, inda ya fayyace yadda hukumar leken asiri ta Amurka ta ba da rashawa don yin tasiri kan wasu ‘yan jarida don su samar da labaran da take so. Hakan ya sa aka yi tunanin cewa, labaran wai Sin take da laifin yada kwayar cuta ko kwayar cuta ta fito daga dakin gwajin kwayoyin hallitu na Wuhan, labaran da wasu kafofin yada labarai da hukumar ke da tasiri kansu ne suka bayar. Saboda hukumar leken asiri ta Amurka ta taba amince cewa, shirin “Operation Mockingbird” na yin tasiri kan a kalla ‘yan jarida 400 da manyan kungiyoyi 25.

To, ganin yadda sassan leken asiri na Amurka suke yin karya da yaudara, shi ya sa gwamnatin Amurka ta bukaci sassan leken asiri da su gudanar da binciken gano asalin kwayar cutar, saboda burin wasu ‘yan siyasar kasar da ba shi da alaka da hakikanin gaskiya bisa kimiyya game da batun asalin cutar, a maimakon haka, suna son fitar da wani sakamako dake iya gamsar da su ne kawai. Shin ko za a amince da irin wannan sakamakon da za su bayar? (Amina Xu)