logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Aikin binciken asalin kwayar cutar COVID-19 na bukatar hadin-gwiwa maimakon shafawa wasu bakin fenti

2021-08-24 20:42:37 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Aikin binciken asalin kwayar cutar COVID-19 na bukatar hadin-gwiwa maimakon shafawa wasu bakin fenti_fororder_src=http___download_zjgkw_org_46-2004230921190-L_jpeg&refer=http___download_zjgkw

Mai magana da yawun fadar White House ta kasar Amurka Jen Psaki ta bayyana cewa, za’a kammala aikin rubuta rahoto kan binciken asalin kwayar cutar COVID-19 da shugaba Joe Biden ya bukaci hukumar leken asirin kasar ta yi, amma ana bukatar wasu karin kwanaki don fitar da rahoton da babu wani sirri a ciki. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, binciken asalin kwayar cutar, yana bukatar hadin-gwiwa, maimakon shafawa sauran kasashe bakin fenti.

Wang ya ce, binciken asalin cutar ya dogara kan tsari na kimiyya ba asirin da aka leko ba. Bukatar hukumomin leken asiri su binciki asalin cutar, ba ta mutunta kimiyya ba. Hukumomin leken asirin Amurka sun dade suna aikata laifuffuka, kuma rahoton da za su fitar game da binciken asalin kwayar cutar, ba zai kunshi gaskiya ba, rahoto ne maras kwararan shaidu da ya shafawa sauran kasashe bakin fenti.

Wang ya kuma bukaci Amurka ta daina dorawa sauran kasashe laifi da shafawa kasar Sin bakin fenti, ta kuma bayyanawa duniya alkaluman yawan mutanen da suka kamu sanadiyar cutar tun farkon bullar ta a kasar, da gaggauta gayyatar kwararrun WHO su je Amurka don gudanar da bincike kan asalin cutar, da bayyana gaskiyar lamarin bisa kimiyya da adalci ga duk duniya da ma al’ummar Amurka. (Murtala Zhang)