logo

HAUSA

Bai kamata a lalata batun gano asalin kwayar cutar COVID-19 ba

2021-08-27 14:42:49 CRI

Bai kamata a lalata batun gano asalin kwayar cutar COVID-19 ba_fororder_210827-Faeza4-Onunaiju

Daraktan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin a Nijeriya, Charles Onunaiju, ya ce ya kamata binciken asalin cutar ya kasace ba tare da wata manufa ta siyasa ko kishi ko neman nuna karfi ba.

Daraktan ya bayyana haka ne yayin wani taron karawa juna sani mai taken “Rigakafin COVID-19: tabbatar da rabonsa bisa adalci da daidaito”, wanda Mujallar Diplomats Extra Magazine ta shirya a Abuja.

Da yake gabatar da jawabi, Daraktan cibiyar binciken harkokin doka ta Sin da Afrika a Jami’ar Abuja, Farfesa Sheriff Ghali, ya ce hadin gwiwa kan allurar rigakafi karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya wata dabara ce ta karfafa hadin gwiwar kasa da kasa wajen dakile kwayar cutar.

A cewarsa, kimanin kasashe 140 ne suka amince da shawarar, kana cikinsu akwai kasashen Afrika 40, inda kuma kasashe sama da 100 suka amince da rigakafin kasar Sin bisa la’akari da cewa, hukumar lafiya ta duniya ta sahale amfani da shi. (Fa’iza Mustapha)