logo

HAUSA

Johnson da Biden sun yi alwashi aiki tare game da yanayin da ake ciki a Afghanistan bayan Taliban ta karbe iko

2021-08-18 11:02:39 CRI

Johnson da Biden sun yi alwashi aiki tare game da yanayin da ake ciki a  Afghanistan bayan Taliban ta karbe iko_fororder_210818-Ahmad3-Joe Biden and Boris

Firaministan Birtaniya Boris Johnson, da shugaban kasar Amurka Joe Biden, sun tattauna ta wayar tarho da yammacin ranar Talata game da halin da ake ciki a Afghanistan bayan da Taliban ta karbe ragawar shugabancin kasar, fadar Downing Street ta bayyana cikin wata sanarwa.

Shugabannin biyu sun amince da yin hadin gwiwa tsakaninsu a ’yan kwanakin nan domin taimakawa wajen kwashe ’yan kasashensu, da suka kumshi ma’aikatansu na yanzu da tsoffin ma’aikata, da sauran mutane daga kasar ta Afghanistan.

Johnson da Biden, sun kuma amince ga sauran kasashen duniya da su hada gwiwa wajen magance fuskantar tabarbarewar yanayin jin kan bil adama a kasar ta Afghanistan.

Birtaniya tana shirin kara yawan tallafin jin kai zuwa shiyyar da kuma sake tsugunar da ’yan gudun hijira.

Ofishin al’amurran cikin gidan Birtaniya ya sanar a daren Talata cewa, sama da ’yan gudun hijirar Afghanistan 20,000 za a baiwa damar zama a kasar Birtaniya a sama da shekaru biyar.

A hirarsu ta wayar tarho, shugabannin biyu sun kuma amince a shirya taron kungiyar kasashen G7 ta kafar bidiyo nan da wasu kwanaki masu zuwa domin tattauna halin da ake ciki a Afghanistan. (Ahmad Fagam)