logo

HAUSA

Ziyarar Biden a Turai ta nuna hakika alaka tsakanin Amurka da kasashen Turai ba ta da inganci

2021-06-18 20:29:54 CRI

Ziyarar Biden a Turai ta nuna hakika alaka tsakanin Amurka da kasashen Turai ba ta da inganci_fororder_618

A makon da ya gabata, an kira taron kolin G7 da taron kolin NATO da kuma taron kolin Amurka da kasashen Turai, yayin wadannan taruka, an ga matakan da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya dauka yayin ziyararsa ta farko da ya yi a kasashen Turai tun bayan da ya kama mulki, wato yunkurinsa na yin adawa da kasar Sin ta hanyar kafa kawancen kasarsa a Turai, amma wane irin amsa ne kasashen Turai suka bai wa Amurkawa?

Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta bayyana ra’ayinta a gun taron kolin G7, inda ta bayyana cewa, duk da cewa akwai sabani tsakanin kasarta da kasar Sin da kuma Rasha, amma rukunin G7 yana fatan zai gudanar da hadin gwiwa da kasashen biyu, musamman ma a bangaren dakile sauyin yanayi da kare muhalin hallitu. Kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron shi ma ya yi tsokaci cewa, rukunin G7 ba kungiya ce dake yin adawa da kasar Sin ba, haka kuma yana fatan zai yi kokari tare da kasar Sin domin daidaita batutuwan dake shafar sauyin yanayi da cinikayyar kasa da kasa da manufofin raya kasa da sauransu.

A bayyane take cewa, manyan kasashen biyu wadanda ke taka rawar jagoranci a nahiyar Turai wato Jamus da Faransa ba su so su bi shawarar Amurka, kuma sun nuna ra’ayinsu kai tsaye. A halin yanzu, Amurka da kasashen Turai suna dogaro da juna ne domin tabbatar da tsaro, duk da sabani da dama dake tsakanin sassan biyu, lamarin da ya sa ake ganin alakar dake tsakaninsu ta gamu da matsala.(Jamila)