logo

HAUSA

MDD ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa fararen hula a jamhuriyar Nijar

2021-08-19 10:54:02 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da kakkausar murya, kan harin nan na ranar Litinin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai wa wasu fararen hula a yankin Tillaberi na jamhuriyar Nijar.

Mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, Guterres ya kuma mika sakon ta’aziya ga iyalan wadanda harin ya shafa, tare da bayyana damuwa matuka kan tasirin da yawaitar irin wadannan hare-hare, ka iya yi kan yanayi na jin kai a yankin na Tillaberi, inda tuni sama da mutane 100,000 suka rasa muhallansu, kana wasu 520,000 suke neman taimakon jin kai.

Babban sakataren MDDr ya nanata kudirin MDD, na ci gaba da goyon bayan jamhuriyar Nijar, a kokarin da take yi na dakile da kuma yakar ayyukan ta’addanci, da tsattsauran ra’ayi, da inganta zamantakewar al’umma da samun ci gaba mai dorewa.(Ibrahim)

Ibrahim